Dubun wasu tsagerun yan bindiga da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara ya cika
- Wasu mutum hudu da ake zargin manyan tsagerun yan bindiga ne sun shiga hannu a jihar Sokoto
- Kwamandan rundunar NSCDC yace an gayyaci wani babban mutum wanda ake zargin yana da alaka da ɗaya daga cikin waɗanda aka kama
- Rahoto ya tabbatar da cewa daga cikin mutanen da suka shiga hannu akwai yan leken asirin yan bindiga
Sokoto- Haukumar tsaro (NSCDC), ranar Laraba, ta sanar da kame wasu tsagerun yan bindiga guda huɗu a jihar Sokoto.
Channelst tv ta ruwaito cewa waɗan da ake zargin mambobin manyan ƙungiyoyin yan bindiga ne da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara.

Asali: UGC
Jami'ai sun damke mutanen ne bisa zargin hannu a garkuwa da manyan mutane, fashi da makami, satar dabbobi da kuma kashe mutane a wasu yankunan waɗan nan jihohi biyu.

Kara karanta wannan
Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane
An gayyaci wani babban mutum
Kwamandan jami'an NSCDC reshen jihar Sokoto, Mohammed Saleh-Dada, yace wasu daga cikin mutanen da aka damke yan leken asirin yan bindiga ne.
A cewar kwamandan hukumarsu ta gayyaci wani babban mutum da ake zargin yana da alaƙa da ɗaya daga cikin mutanen da aka kame.
Yace:
"Mun gayyaci wani sanannen mutum a yankin karamar hukumar Dange/Shuni, jihar Sokoto, bisa zargin yana da wata alaƙa da mutum daya da ake zargi."
Mahara sun kai sabon hari Kaduna
A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane
Wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun hallaka mutum 8 a wani sabon hari da suka kai kauyukan karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan
Wata Sabuwa: Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Kibori da kuma Atagjah, a karkashin yankin Aytap a kudancin jahar Kaduna.
Asali: Legit.ng