Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta amince Shugaba Buhari ya sake karban bashin $16bn da €1bn

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta amince Shugaba Buhari ya sake karban bashin $16bn da €1bn

  • Yan majalisar dattawa sun amince da sabbin basussukan da gwamnatin tarayya ke shirin karba
  • Mambobin Majalisar a baya sun yi Alla-wadai da shirin karban bashin $700 million da gwamnatin tarayya ke shirin yi
  • Sanatocin yanzu sun bayyana cewa wadannan basussuka zasu taimaka wajen kawowa Najeriya cigaba

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya a ranar Laraba ta amince da Shugaba Muhammadu Buhari ta sake karban wasu basussukan $16,230,077,718, da €1,020,000,000 daga kasar waje.

Hakazalika majalisa ta amince da wani bashin tallafi daban na $125 million, rahoton ChannelsTC.

Bankin duniya, Bankin China, bankin masana'antu, da wasu bankuna irinsu bankin cigaban Afrika AfDB.

Majalisar ta amince da amsan wadanann basussukan ne biyo bayan rahoton majalisar dattawa na basussuka karkashin jagorancin Sanata Clifford Ordia.

Sanata Ordia ya bayyana cewa tun shekarar 2018-2020 aka shirya karban wadannan basussuka don wadannan ayyuka.

Kara karanta wannan

Hotunan jama'ar Anambra suna tururuwar karbar katikan zabensu kafin Asabar

Dan majalisan ya bayyana cewa wadannan ayyuka zasu taimaka wajen farfado da kasuwancin da jin dadin jama'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari zzai sake karban bashin $16bn da €1bn
Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta amince Shugaba Buhari ya sake karban bashin $16bn da €1bn Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

Sakatariyar din-din-din ta ma'aikatar ruwan sha, Mrs Esther Didi Walson-Jack, ta bayyana gaban Kwamitin Mambobin majalisar dattawa kan basussukan gida da waje ranar Laraba.

Mrs Esther ta gurfana gaban Sanatocin ne don bayani kan bukatun basussuka da ma'aikatar ta gabatar a kasafin kudin 2022 da shugaba Buhari ya kai, rahoton Thisday.

Tace gwamnatin zata karbi bashin ne don samar da isasshen ruwan sha ga yan Najeriya a karkara da birane karkashin shirin SURWASH.

A bayanin da tayi, tace za'a yi amfani da kudin tsawon shekaru biyar da wannan aiki.

Ta kara da cewa daga cikin kudin, za'a yi amfani da $640 million wajen ainihin aiki yayinda za'a yi amfani da $60 million domin horar da ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng