'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi
- Wasu ‘yan bindiga sun kai wa mazauna karamar hukumar Batsari a jihar Katsina hari a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba
- An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kona gidaje da dama tare da bin gida-gida suna kashe mutane da cin zarafinsu
- Dan majalisar dokokin Katsina mai wakiltar Batsari, Hon Jabir Yauyau ne ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari
Katsina - Ana fargabar 'yan bindiga sun kashe mutane da yawa tare da kona dukiyoyinsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan wasu al'ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Harin wanda rahotanni suka ce ya fara ne da yammacin ranar Talata zuwa sanyin safiyar Laraba, yayi sanadiyyar kona gidaje da yawa da suka hada da gine-ginen gwamnati da motoci, Daily Trust ta ruwaito.
Shaidu sun ce akalla al’ummomi biyar ne ‘yan bindigar suka afkawa, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata ba.
Wata majiya ta shaida cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A cikin kowace yankin da suka mamaye, 'yan bindigar sun yi ta harbe-harbe ta iska domin nuna alamar shigowarsu kafin su fara shiga gida zuwa gida, suna wawashe dukiyar mutane tare da cin zarafin mazauna."
Wata majiya daga jaridar The Guardian da ke da masaniya kan lamarin ta ce ‘yan bindigar sun harbe mutane bakwai har lahira, yayin da wasu da dama suka jikkata a yayin harin.
An yi ta rade-radin cewa daya daga cikin wadanda aka kashe a harin lauya ne mai suna Barr Nura Hassan Wagine amma dai ba a tantance gaskiyar batun ba.
Majiyar ta kara da cewa da dama daga cikin wadanda harin ya rutsa da su na kokarin tserewa daga harin da ‘yan bindigan suka kai musu yayin da suka samu munanan raunuka.
A lokacin da aka tuntubi dan majalisar da ke wakiltar Batsari a majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Jabir Yauyau, ya ce ya samu labarin faruwar lamarin, amma har yanzu yana tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru.
Ya kara da cewa, zai yi wuya a samu cikakken bayanin abin da ya faru a yanzu, saboda katse hanyoyin sadarwa da aka yi a yankin.
Ya kuma ce:
“An sanar dani game da yawancin wadanda aka kashe. Mutane ne da na sani da kaina, amma har yanzu ina bukatar tabbatarwa.
"Ina kokarin tabbatar da abin da ya faru a zahiri saboda zan gabatar da kudiri a kan al'amuran da suka shafi mahimmancin jama'a a majalisa, amma dole ne in sami ainihin bayani."
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ba.
Miyagun ‘yan bindiga sun budewa motar 'yan sanda wuta a Zamfara, sun bindige da dama
Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13
A wani labari mai kama da wannan, wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda akalla bakwai a wani kwanton bauna da suka kai a kusa da kauyen Zonai da ke gundumar Magami a karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Jami'an na dawowa ne daga bakin aiki inda a ranar Litinin a wani shingen binciken ababan hawa da ke kusa da kauyen Zonai da ke kan titin Gusau-Magami-Dansadau, a lokacin da ‘yan bindigar suka bude wuta kan motar da ke dauke da jami’an.
Wani mazaunin yankin mai suna Halliru ya shaida cewa:
“Wannan lamari ne na matukar bakin ciki musamman a gare mu 'yan garin Magami saboda ‘yan sanda sun taimaka matuka wajen tabbatar da dakile munanan yanayin tsaro a wannan yanki.”
Asali: Legit.ng