Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun bude wa mayakan ISWAP wuta a kan hanyar Maiduguri

Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun bude wa mayakan ISWAP wuta a kan hanyar Maiduguri

  • Rahotanni sun bayyana cewa an yi dogon musayar wuta tsakanin mayakan Boko Haram/ISWAP da Sojoji a Maiduguri
  • Wani direba ya bayyana cewa dole tasa suka yi cikin daji da motocin su yayin da suka jiyo ƙarar harbe-harbe
  • A makon da ya gabata mayakan ISWAP sun sace matafiya aƙalla 10 a hanyar kafin sojoji su tarwatsa su

Borno - The Nation ta rahoto cewa an yi batakashi tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Boko Haram/ISWAP a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Wata majiya daga cikin jami'an tsaron, ya bayyana cewa musayar wutan ta yi sanadiyyar tara matafiya da dama a kan hanya.

Ya kuma kara da cewa mintuna 30 kacal ya ɗauki dakaraun sojin su samu nasarar fatattakar yan ta'addan daga wurin.

Dakarun soji
Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun bude wa mayakan ISWAP wuta a kan hanyar Maiduguri Hoto: infotrustng.com
Asali: UGC

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

"Boko Haram/ISWAP sun fito tsakanin Maita Kulurri da Ngamdu, suka bude wa jami'an soji wuta. Sojojin sun maida martani, kuma suka samu nasarar tarwatsa su."

Wane hali matafiya suka shiga a kan hanya?

Wani direba mai suna Sani ya tabbatar da faruwar lamarin, yace an dakatar da motarsu kafin su ƙarasa sansanin sojoji na Ngamdu.

A cewar direban wasu abokan aikinsa da dama sun fantsama daji saboda tsorata da musayar wutan da ake yi.

Sani yace:

"Muna kan hanyar zuwa Maita Kuluri yayin da muƙa fara jin karar harbin bindiga, nan fa muka fara gudu cikin jeji, wasu ma da mota suka shiga jejin."
"Mun shafe minti 40 a cikin jejin kafin wasu su fara fitowa kan hanya. Yayin da muke tafiya naga wata mota an ƙona ta, amma bani da tabbacin motar sojoji ce ko ta yan ta'adda."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a makon da ya gabata yan ta'addan sun sace matafiya 10 kafin sojoji su dakile yunƙurin su.

Kara karanta wannan

Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger

A wani labarin na daban kuma barayin da suka sace masu ibada 60 a Kaduna sun bukaci buhunan shinkafa da jarkokin mai

Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun yi barazanar cewa matukar ba'a gaggauta kai musu kayan abincin nan ba to zasu bar mutanen cikin yunwa.

Shugaban ƙungiyar kiristoci (CAN) reshen jihar Kaduna, John Hayab, ya shaida wa manema labarai cewa ɓarayin suna neman a basu maƙudan kuɗaɗe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262