Miyagun ‘yan bindiga sun budewa motar 'yan sanda wuta a Zamfara, sun bindige da dama
- 'Yan bindiga a jihar Zamfara sun hallaka jami'an 'yan sanda a wani kwanton bauna da suka kai musu a wani yankin jihar
- An ce sun bindige jami'an 'yan sanda bakwai, kuma tuni an kai gawarwakinsu asibiti don ci gaba da bincike
- Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ba
Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda akalla bakwai a wani kwanton bauna da suka kai a kusa da kauyen Zonai da ke gundumar Magami a karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Jami'an na dawowa ne daga bakin aiki inda a ranar Litinin a wani shingen binciken ababan hawa da ke kusa da kauyen Zonai da ke kan titin Gusau-Magami-Dansadau, a lokacin da ‘yan bindigar suka bude wuta kan motar da ke dauke da jami’an.
Zaɓen Anambra: Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC ya bayyana dalilin da yasa ya jefa wa Soludu ƙuri'arsa
Wani mazaunin yankin mai suna Halliru ya shaida cewa:
“Wannan lamari ne na matukar bakin ciki musamman a gare mu 'yan garin Magami saboda ‘yan sanda sun taimaka matuka wajen tabbatar da dakile munanan yanayin tsaro a wannan yanki.”
“Hakika, kasancewarsu a wannan shingen binciken ya karawa matafiya kwarin gwiwar bin hanyar. An kashe tare da sace matafiya da dama a hanyar Gusau zuwa Magami mai nisan kilomita 50. Gaskiya abin bakin ciki ne da ban tausayi."
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ba, SP Muhammad Shehu har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na asibitin kwararru na Yariman Bakura, Awwal Usman Ruwandoruwa ya shaida wa Daily Trust cewa an kawo gawarwakin jami’an da aka kashe zuwa asibitin da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata.
Wani dan yankin mai suna Salisu Sani ya shaidawa jaridar Punch cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin lokacin da jami’an ‘yan sanda suka je yankin domin sintiri.
Sani ya ce, ‘yan bindigar sun yi wa jami’an ‘yan sanda kwanton bauna, inda suka kashe bakwai daga cikinsu tare da kona motar da suke aiki.
Sani ya bayyana cewa ‘yan bindigar da ke da yawan gaske sun yi artabu da jami’an ‘yan sanda, inda a sakamakon haka aka kashe jami’an ‘yan sanda bakwai a nan take.
A cewarsa:
“Na ga ana kwashe gawarwakinsu Gusau."
Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna
A wani labarin, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Yobe sun kama wasu matasan Fulani guda biyu da suka datse hannayen juna a wani fada a kauyen Bakin-Ruwa da ke Garin-Alkali a karamar hukumar Bursari a jihar.
Rahotanni sun ce an kama Fulanin biyu suna fada da juna da adduna da sanduna wanda daga baya ya yi muni har da zubar jini, SaharaReporters ta ruwaito.
Mutanen biyu sun datse hannayen juna daga wuyan hannun hagu na kowanne.
Asali: Legit.ng