Babu Farfesa a Najeriya dake samun albashi sama da N416,000: Shugaban ASUU
- Shugaban ASUU na Legas ya bayyana cewa tun shekarar 2009 rabon da a karawa Malaman jami'a albashi
- Kungiyar ASUU ta ba gwamnatin tarayya makwanni 3 don cike mata sharuddanta ko suk koma yajin aiki
- A shekarar 2020, Malaman jami'o'in Najeriya sun yi yajin aikin sama da watanni goma
Legas - Shugaban yankin jihar Legas na kungiyar Malaman jami'a a Najeriya ASUU, Dele Ashiru, ya bayyyana cewa babu Farfesan dake karban albashi sama da N416,000 a wata.
Ashiru ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin ChannelsTV, Sunrise Daily, ranar Talata.
Ya yi kira ga Gwamnati ta kara albashin Malaman Jami'a.
Ya ce duk da yarjejeniyar da akayi da gwamnatin tarayya, gwamnati ta ki rattafa hannu kan yarjejeniya run watar Mayu.
A cewarsa:
"Babu Farfesa a Najeriya dake daukan sama da N416,000 a wata matsayin albashi da alawus. Muna cewa a sake tattauna saboda a inganta rayuwan ma'aikata."
"Mambobinmu basu samu karin albashi ba tun shekarar 2009 har ila yau. Ban tunanin akwai wani bangare a kasar nan da ake yiwa wannan wulakanci."
ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta bawa gwamnati wa'adin sati 3
Kungiyar ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya makwanni 3 don cika mata sharuddan da ta gindaya wa gwamnatin, The Nation ta ruwaito.
Ta bayyana wannan kudirin nata ne inda ta ce wajibi ne gwamnatin ta cika mata alkawarran da su ka sa hannu akai tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.
ASUU ta ce in har gwamnatin bata cika sharuddan na ta ba cikin makwanni 3 za ta dauki tsattsauran mataki.
Asali: Legit.ng