Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

  • An yi musayar wuta tsakanin 'yan IPOB da jami'an tsaro a wani yankin da ake zaben gwamna a yau a jihar Anambra
  • Jami'an tsaro da kansu sun bayyana yadda suka yi gumurzu da 'yan IPOB din, wanda a cewarsu ya shafe sama da awa uku
  • An shawarci manema labarai da su gaggauta komawa da baya domin tsira da rayukansu daga hannun 'yan ta'addan

Anambra - Jami’an tsaro na hadin gwiwa a ranar Talata sun yi artabu da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne a garin Ihiala na jihar Anambra.

Yankin karamar hukumar da ake gudanar da zaben na gwamna ya yi kaurin suna wajen tabarbarewar tsaro, wanda ya kai ga sauya zabe a yankin.

Taswirar jihar Anambra | Hoto: vanguardngr.com
Da Duminsa: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe awa uku suna musayar wuta a Anambra
Asali: Twitter

Artabun wanda ya gudana a mahadar Mbosi Osumowu da ke kan iyakar Anambra ya shafe kusan awanni uku ana yi.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

Wakilin jaridar The Nation, wanda ya ci karo da jami’an da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, shige da fice da sauran jami’an tsaro, an bukaci su koma baya domin tsira da rayukansu.

Wani daga cikin 'yan sanda ya yi gargadin cewa:

“Mun kasance a nan tsawon sa’o’i uku da suka gabata muna musayar wuta da su. Gwara ku juya ku bi hanya mafi aminci."

Kafin fara zaben gwamnan, kungiyar 'yan aware ta IPOB ta sanar da dage umarnin zaman gida da ta sanya a jihar, inji rahoton The Guardian.

Duk da haka, ana kyautata zaton an yi zabe lafiya cikin lumana a jihar ta Anambra.

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

A wani labarin, Misis Ngoesina Mabia, wata matar aure a jihar Anambra, ta haifi da namiji sa'o'i bayan da rahotanni sun ce ta zabi Farfesa Charles Soludo, dan takarar jam'iyyar APGA a zaben gwamnan Anambra.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

Kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Pidgin ta ruwaito, matar da mijinta sun sanya wa jaririn da suka haifa sunan Soludo.

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Rt. Hon Uche Victor Okafor, ya ziyarci ma'auratan don ganewa idonsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.