An kaure tsakanin jami'an EFCC da na gidan yari kan wa zai tafi da Maina magarkama
- Kotu a babban birnin tarayya ta yankewa Maina hukucin zaman gidan kaso na tsawon shekaru takwas
- Yayin da aka gama yanke hukunci, jami'an EFCC da na gidan yari sun samu sabanin waye ya kamata ya dauki Maina
- Daga baya an sasanta, an ba jami'an gidan gyaran hali damar tafiya da Maina, wanda kuma hakan aka yi
Abuja - Rikci ya kaure a babbar kotun tarayya da ke Abuja, yayin da jami’an hukumar EFCC suka yi artabu da jami’an hukumar gyaran hali ta Najeriya, kan tsare tsohon shugaban kwamitin fansho, Abdulrasheed Maina, wanda aka yankewa hukunci.
Ko da yake mai shari’a Okon Abang ya yanke wa Maina hukuncin daurin shekaru 8 a gidan yari kuma ya ce Maina ya kasance a gidan yari amma duk da haka jami’an EFCC sun samu sabani da takwarorinsu na gidan yari.
Punch ta ruwaito cewa, jami’an tsaro na EFCC da NCoS sun samu sabani a lokacin da suke kokarin tafiya da Maina.
Bayan yanke hukuncin ne jami’an gidan yarin wadanda tuni suka kasance a shirye a dakin shari'a da kuma cikin harabar kotun, suka tasa Maina a gaba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai rikicin ya fara ne lokacin da jami’an EFCC suka dage cewa dole ne Maina ya shiga motar su. Amma bayan arangamar, an tattaro cewa jami'an gidan yari ne suka tasa Maina a gaba zuwa magarkama, The Cable ta ruwaito.
Mai shari’a Abang ya yanke wa Maina hukuncin daurin shekaru 61 a gidan yari kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi halasta kudaden haram amma kuma zai ci gaba da zama a magarkama na tsawon shekaru takwas.
Kotun ta same shi da laifin sa ma’aikatan bankin Fidelity su bude masa asusun ajiyar banki ba tare da bin hanyar da ta dace ba kana da karkatar da kudade.
Kotu ta yanke wa Maina hukuncin shekaru 8 a gidan yari bayan kama shi da laifin satar N2b
Kunji cewa, Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta kama tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina, da laifin sata da wanke kudin haram zuwa na halas, Premium Times ta ruwaito.
A wani hukunci da Okong Abang, alkalin kotun ya yanke, ya ce kotun ta kama Maina da laifin satar kudi sama da biliyan 2 na 'yan fansho "wadanda da yawansu sun rasu kuma basu ci guminsu ba," alkalin yace.
"Na kama Maina da laifin aikata zargi na 2, 6, 9, 3, 7 da na 10," Abang yace.
Asali: Legit.ng