Dubansa ya cika: An kama sojan da ke da hannu a harin da aka kai har cikin NDA

Dubansa ya cika: An kama sojan da ke da hannu a harin da aka kai har cikin NDA

  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, an kame jami'in sojan da ke da hannu a harin da aka kai makarantar sojoji ta NDA
  • A halin yanzu, an dauko shi daga inda yake aiki a jihar Adamawa zuwa NDA da ke jihar Kaduna domin ci gaba da bincike
  • An kai hari NDA a watan Agusta, lamarin da ya jawo cece-kuce daga bangarori daban-daban a fadin kasar tare da ganin gazawar sojoji

Kaduna - The Nation ta ruwaito cewa, rundunar sojin sama ta kama Torsabo Solomon, wani Sajan da ake zargi da hannu a kai hari a makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA) da ke Kaduna.

An kashe jami’ai biyu, an kuma yi garkuwa da wani jami’i guda a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa NDA hari a watan Agusta.

Kara karanta wannan

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

Da dumi-dumi: An kama soja mai hannu a harin 'yan bindiga a NDA
Sojan da aka kama mai hannu a harin NDA | Hoto: naijanews.com
Asali: Getty Images

Wannan lamarin ya haifar da hargitsi a kasar tare da nuna damuwa game da karuwar rashin tsaro.

Majiyar soja ta shaida wa TheCable cewa an kama Solomon ne a ranar Litinin a NAF’s 153 BSG a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

An ce umarnin kama shi ya fito ne daga IM Yusuf, Manjo Janar kuma kwamandan NDA.

Kafin kama shi, Solomon na hidima a Air Force Comprehensive School da ke Yola.

Ana kuma zargin jami'an da sayar da makamai da alburusai ga 'yan bindiga da masu aikata laifuka.

Bayan kama shi, an ce an kai shi NDA da ke Kaduna domin ci gaba da bincike.

Dangane da harin na NDA, fadar shugaban kasar ta bayyana lamarin a matsayin wani yunkuri da aka yi da gangan don bata kokarin gwamnati da kuma ragewa sojoji kwarin gwiwa a yakin da suke yi da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

Rundunar sojin sama ta karyata rahoton kame Sajan Solomon

A bangarenta, cibiyar horas da sojoji ta Najeriya ta musanta kama wani jami'in nata Sajan Torsabo Solomon, wanda aka ce yana da hannu a harin NDA.

A wata sanarwa da NDA ta fitar a daren ranar Litinin ta bakin Manjo Bashir Jajira ta ce jami'in ba ya hannunsu.

Jaridar Punch ta ruwaito inda sanarwar ke karin haske kan batun da cewa:

“Cibiyar horas da sojoji ta Najeriya makarantar horas da sojoji ce ba hukumar tsaro ta bincike ba. Ana shawartar jama'a da su yi watsi da wannan mummunan labari kuma su koma ga Hukumomin Tsaron da suka dace don samun bayani.
"Kwamitin tsaro na Najeriya na son tabbatar wa da jama'a cewa za a kama wadanda suka yi ta'asar tsaro a harabar makarantar horas da sojoji ta Najeriya nan ba da jimawa ba."

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Bayan harin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Cibiyar Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) a Kaduna zai taimaka wajen kara azama, kaimi da sa karfin soji wajen kawo karshen tashin hankali a kasar.

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

"Wannan mummunan aikin zai hanzarta kawar da munanan abubuwan da ke faruwa, wanda membobin rundunar sojin suka kuduri aniyar aiwatarwa cikin kankanin lokaci."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.