Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe
- Yan bindiga karkashin shugabansu Turji sun nada kwamandojinsu a matsayin dagatai a karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto
- Sabbin dagatan da aka nada sun bada umurin bude kasuwanni da gwamnatin Sokoto ta rufe da ma masallatai
- Har wa yau, sabbin dagatan da yan bindigan suka nada sun bawa mutanen gari umurnin su fara tattara musu haraji na miliyoyi
Sokoto - Yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.
Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.
Tsumagiyar Kan Hanya: Barayin da suka sace masu ibada 60 a Kaduna sun bukaci buhunan shinkafa da jarkokin mai
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Manyan kwamandojin Turji guda biyar ne suka hallarci taron, sun hada da Ɗan Baƙƙwalo, Boka Tamisƙe, Hassan Ɗan Ƙwaro, Dogo da Jammu Baƙi.
Daga nan manyan kwamandojin suka umurci mutane su zabi shugabansu daga cikin kwamandojin yan bindigan.
Yan kauyen sun zabi Dan Bakkwalo, daga bisani aka basu dokoki da za su rika bi.
Da ya ke karanto musu sabbin dokoki, Dakkwalo ya ce daga yanzu babu wani dan sanda, soja ko dan sa-kai da za a bari ya shiga garin.
Ya umurci mutane su rika kawo masa kara idan wani matsala ya tashi a tsakaninsu.
Sabon shugaban ya umurci mutanen su tara masa N1.5m a matsayin zakka.
Nan take Dan Bakkwalo ya bada umurnin a bude masallacin Juma'a da kasuwannin (Talata-Talata) da ake ci a garin Gangara da gwamnatin Sokoto ta rufe.
Dan Bindiga ya nada kansa hakimi
A kauyen Makwaruna, shugaban yan bindiga Boka Tamiske ya nada kansa hakimi sannan ya kira taro inda ya sauke tsohon hakimin wani Dan Sani ya fadawa mutane shine shugaba.
Dan Sani ya shaidawa mutanen gari cewa Boka ne sabon hakiminsu.
Daya daga cikin mazauna kauyen ya shaidawa jaridar cewa:
"Mutanen garin ba su da wani zabi illa yi wa yan bindigan biyayya."
"Yanzu sune ke kula da garin, wurinsu ake zuwa idan ana bukatar warware wata matsala."
Kazalika, an saka wa mutanen kauyuka 85 harajin N300,000 a kauyukan Burkusuma saboda rashin noma isassun abinci da yan bindigan za su yi amfani da shi.
An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa
A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.
Kano: An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi
An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.
A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.
Asali: Legit.ng