Zuwa yanzu INEC ta karbi sakamakon zaben kananan hukumomi 19 cikin 21
- A ci gaba da karbar sakamakon zabe na jihar Anambra, hukumar INEC ta ce ta karbi sakamakon zabe na kananan hukumomi 19
- An tattara sakamakon ne, inda hukumar ta zauna domin karbarsa daya bayan daya daga jami'an tattara sakamako
- A halin an tafi hutu, ana sa ran za a dawo domin bayyana karbar sauran na kananan hukumomi biyu
Anambra - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da karbar sakamakon zaben kananan hukumomi 19 na jihar daga cikin 21, The Nation ta ruwaito.
Sauran biyun kuma a cewar Hukumar ana dakon su kuma za su isa Hukumar da ranar yau din nan.
Mista Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa, mai kula da kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ne ya sanar da hakan da safiyar Lahadi a ofishin hukumar da ke Awka.
Ko da yake bai ambaci kananan hukumomin biyu da suka rage ba, ya ce za a fara sanar da sakamakon kananan hukumomin da karfe 11 na safe.
Sai dai kuma an shirya fara fitar da sakamakon zaben gwamnan Anambra, wanda aka gudanar ranar Asabar a jihar.
Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku
A wani labarin, Jam’iyyar APGA ta lallasa jam'iyyar tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, da Sanata Uche Ekwunife, a karamar hukumarsu, This Day ta ruwaito.
Dukansu ‘yan karamar hukumar Anaocha ne, kuma ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne. Shi ma dai Sanata Victor Umeh ya fito daga karamar hukumar.
Dokta Okene Isaac, malami a Jami’ar Calabar, wanda shi ne jami’in tattara bayanan kananan hukumomi ya ce: “Jimillar masu kada kuri’a 109860, sun amince da kada kuri'u 15940."
Asali: Legit.ng