Soludo na APGA ya bi yan takaran APC da PDP har garuruwansu ya lallasa su
- Charles Soludo ya samu gagarumin nasara a karamar hukumar Aguata ta jihar
- Ya samu jimillar kuri'u 9,136, yayinda Andy Uba da Ozigbo ko kamo kafar kuri'unsa basu yi ba
- Wannan shine karamar hukuma ta bakwai da Soludo ke kan gaba wajen nasara a zaben
Anambra - Dan takaran jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Charles Soludo, ya bi manyan abokan hamayyarsa karamar hukumarsu kuma ya lallasa su.
Charles Soludo ya lallasa Andy Uba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Aguata.
Daga cikin gundumomi 20 dake karamar hukumar Aguata, Soludi ya kashe Isuofia, Nkpologwu, Igbo-Ukwu I/II, Ekwulobia II, Umuchu I da II, dss, rahoton Premium Times.
Ya samu jimillar kuri'u 9,136, yayinda Andy Uba ya samu 4,773 kuma Ozigbo ya samu 3,798.
A cewar baturen zabe karamar hukumar Aguata, Alim Ajake, ba'a yi zabe a wasu rumfunan zabe a gundumomi hudu ba, rahoton ya kara.
Wannan sun hada da Umuchu I (Mutum 2,292), rumfunan biyu a Ekwulobia II, rumfuna uku a Igbo-Ukwu I, da rumfuna biyar a Igbo-Ukwu II
Ga Sakamakon zaben kamar yadda aka sanar:
Adadin wadanda sukayi rijista – 14,4766
Adadin wadanda aka tantance – 20,809
A – 111
AA – 07
AAC – 73
ADC – 32
ADP – 91
APC – 4,773
APGA – 9,136
APM – 40
APP – 11
BP – 22
LP – 132
NNPP – 11
NRM – 30
PDP – 3,798
PRP – 31
SDP – 60
YPP – 1,070
ZLP – 120
Adadin sahihan kuri'u: 19,548
Adadin kuri'un da akayi watsi da su: 654
Asali: Legit.ng