Zaben Anambra: Dan takaran APGA ya lashe zabe a kananan hukumomi 11 cikin 21 kawo yanzu
- Dan takaran jam'iyyar APGA a zaben dake gudana yanzu haka a Anambra ya dau hanyar lashe zabe
- Bisa sakamakon da aka tattara kawo yanzu a jihar, Farfesa Charles Soludo ke kan gaba kuma da tazara mai yawa
- Daga shi sai dan takaran jam'iyyar PDP, sannan kuma na APC
Charles Chukwuma Soludo na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya lashe zaben kananan hukumomi goma sha daya kawo yanzu da ake cigaba tattara kuri'un da aka kada.
Kananan hukumomin sun hada da Awka South, Onitsha South, Orumba South, Anaocha, Anambra East, Njikoka, Orumba North, Aguwata, Oyi, Ayamelum, da Dunukofia.
Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da cewa za'a cigaba da tattara sakamakon zaben ranar Lahadi.
Akwai kananan hukumomi 21 a jihar Anambra amma sakamakon 11 kadai aka sanar.
Kawo yanzu, Charles Soludo na da jimillar kuri'u 74,859 daga kananan hukumomin 11, yayinda dan takaran PDP, Valentine Ozigbo na PDP ke biye da shi da kuri'u 30,581 sannan Andy Uba na APC mai kuri'u 26,056
Ga jerin sakamakon:
Njikoka LGA
APC - 3,216
APGA - 8,803
PDP - 3,409
YPP - 924
Awka South
APC – 2595
APGA – 12891
PDP – 5489
Onitsha South LG
APC – 2050
APGA – 4281
PDP – 2253
Orumba South
APC: 2,060
APGA: 4,394
PDP: 1,672
YPP: 887
Anambra East LGA
APC 2034
APGA: 9746
PDP: 1380
Anaocha LGA
APC – 2085
APGA – 6911
PDP – 5,108
Orumba North
APC – 2692
APGA – 4826
PDP – 1863
Aguwata
APC – 4773
APGA – 9136
PDP – 3798
Dunukofia
APC - 1991
APGA -4124
PDP - 1680
Oyi
APC - 2830
APGA - 6133
PDP - 2484
Ayamelum
APC - 2409
APGA - 3424
PDP - 2804
Asali: Legit.ng