Da duminsa: Dan takaran jam'iyyar APC, Sanata Andy Uba, ya lashe akwatin rumfarsa
- Sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra sun fara shigowa yan awanni a wasu rumfunan zabe
- Na farko-farkon shine akwatin rumfar dan takaran jam'iyyar APC, Sanata Andy Uba
- A akwatinsa, Jam'iyyar PDP kuri'u biyu kacal ta samu yayinda mafi yawa shine APGA
Awka - Dan takaran kujeran gwamnan jihar Anambra karkashi jam'iyyar All Progressives Congress APC, Sanata Andy Uba, ya lashe akwatin rumfar da ya kada kuri'arsa.
Andy Uba ya yiwa abokan hamayyarsa dukan kawo wuka inda babu wanda ya kamo kafarsa a wannan akwati.
Kamar yadda baturen zaben akwatin ya sanar jam'iyyar APC ta samu kuri'u 80, yayinda mafi kusa da hakan shine APGA wanda ya samu kuri'u 10, rahoton Premium Times.
Daga ita kuma sai jam'iyyar YPP da ta samu kuri'u 5, sai kuma jam'iyyar PDP da Accord suka samu kuri'u 2.
A karshe jam'iyyun AAC, LP, SDP sun samu kuri'u daya-daya
Ƙuri'ar jin ra'ayi da wani kamfanin Amurka yayi ya nuna jam'iyyar da za ta lashe zaɓen gwamna
Wani kamfani na shawarwari akan harkokin siyasa da gudanar da bincike na kasa da kasa da ke Amurka ya ce akwai yiwuwar Andy Uba na jam’iyyar APC ya lashe zaben da za a yi na gwamnoni a Anambra na ranar 6 ga watan Nuwamba.
Bisa ruwayar The Punch, kamfanin na bincike ya gudanar da kuri’ar jin ra’ayi wacce gidauniyar ‘Power to the People’ ta aiwatar akan ‘yan takara 6 kuma manuniya ta nuna wanda zai iya ci nasara.
A cikin ‘yan takarar akwai Godwin Maduka na jam’iyyar Accord, Charles Soludo na APGA, Valentine Ozigbo na PDP, Obiora Okonkwo na ZLP da kuma Sanata Andy Uba na jam’iyyar APC.
Rahotonni sun fi mayar da hankali akan ‘yan takarar gwamnan guda biyu, Soludo da Uba, inda ya kula da cewa dan takarar APC zai iya cin nasara da tazarar 3 zuwa 4% a zaben mai zafi da za a gudanar.
Asali: Legit.ng