Danjuma Goje ne ya kawo yan kalare Gombe, ba hari aka kai masa ba, Gwamnatin jihar
- Gwamnan jihar Gombe ya yi Alla-wadai bisa abin da ya auku ranar Juma'a yayinda Sanata Danjuma Goje ke niyyar shiga jihar
- Kwamishanan Labaran jihar yace Sanatan ne ya taho da matasa rike da muggan makamai cikin jama'a
- A cewarsa, ko makon da ya gabata tsohon Gwamnan ya yi irin hakan, hakazalika lokacin babbar Sallah
Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta caccaki tsohon gwamnanta kuma Sanata mai wakiltan mazabar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje, bisa rikicin da ya auku cikin jihar.
Kwamishanan labaran jihar, Julius Ishaya Lepes, a jawabin kar ta kwana da ya saki da yammacin Juma'a ya bayyana cewa Sanata Goje da kansa ya haddasa wannan rikicin.
Yace dama halin tsohon gwamnan ne tattara yan kalare duk lokacin duk zai shigo jihar.
Yace:
"Tsohon gwamnan kamar yadda ya saba ya tattaro yan kalare daga kananan hukumomi daban-daban da sunan masu rakiyansa zuwa cikin garin Gombe."
"Hakazalika makon da ya gabata a Deba, karamar hukumar Yamaltu Deba irin haka ta faru."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gwamnan jihar bayan taya iyalan wadanda rikicin ya shafa jimami ya jinjinawa jami'an tsaro bisa aikin da sukayi na kwantar da kurar da sukayi."
Danjuma Goje ne ya kawo yan kalare Gombe
Gwamnatin ta kara da cewa har yanzu Goje ya lashe takobin tura yan kalare hana jama'a sakat da zaman lafiya.
Tace ba zata zuba ido wasu yan siyasa su tayar da rikici cikin jihar da zai haddasa asarar rayuka ba.
Yace:
"Abin takaici har yanzu Goje bai tuba ba kuma ya lashi takobin dawo da yan kalaren da ya samar don tada hankulan al'umma a jihar Gombe."
"Gwamnati ba zata zuba ido wasu yan siyasa su haddasa rikicin da zai shafi jama'a ba ko ya kai ga asasar rayuka."
Yan daba hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone
Mun kawo muku cewa wasu da ake zargin yan daba ne, a ranar Juma'a, sun hana Sanata Muhammad Goje shiga garin Gombe.
Goje, wanda ya tafi Gombe domin halartar daurin aure, ya dira a filin saukan jirage na Gombe a Lawanti misalin ƙarfe 10.40 na safe.
Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda ake zargi yan daban ne sun tare babban titin Gombe-Bauchi kusa da International Conference Centre, sun cinna wuta a titi sun hana shiga ko fita daga Gombe.
Asali: Legit.ng