Sabon hoton Mufti Menk sanye da babbar riga ya janyo cece-kuce

Sabon hoton Mufti Menk sanye da babbar riga ya janyo cece-kuce

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani sabon hoton shahararren malamin nan na duniya, Mufti Isma'il Menk
  • A cikin hoton, an gano malamin sanye da dinkin babbar riga wacce ta sha aiki da kuma hula zanna bukar
  • Mutane da dama musamman mata sun yaba da irin kyawu da Shehin Malamin yayi a cikin irin wannan shiga da ba a taba ganinsa da ita ba

Wani sabon hoton shahararren Malamin nan na addinin Musulunci na duniya, Mufti Isma'il Menk, ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan soshiyal midiya.

A cikin hoton wanda shafin Instagram na northern_hibiscuss ta wallafa, an gano Shehin Malamin sanye da dinkin babbar riga wacce ta ji aiki da kuma hula zanna bukar.

Sabon hoton Mufti Menk sanye da babbar riga ya janyo cece-kuce
Sabon hoton Mufti Menk sanye da babbar riga ya janyo cece-kuce Hoto: northern_hibiscuss
Asali: Instagram

Malamin ya fito shar da shi kasancewar ba a taba ganin shi cikin irin wannan shiga ba, domin an saba ganinsa ne sanye da farar jallabiya.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

Shafin na northern_hibiscuss ta sanya hoton ne dauke da rubutu kamar haka:

"@muftimenkofficial gaskiya da gangan yayi wannan hoton.
"Da jallabiyar sa ma matan arewa sun mace bare yaci baban riga da zanna bukar?
"Kun tuna kwanaki wata har an saka rana tayi cancelling ita se mufti? Har yazo page din mu ya bata hakuri?
"Lol yanzu za ku fara ganin shi a gaban hausa novel a kasuwar rimi. Fari, ga kasumma ga iya kira'a asali jikan larabawa ne. Ga iya lafazi hanci kamar biro hakwara kamar madara."

Tuni dai mabiya shafin musamman mata suka fito domin tofa albarkacin bakunansu

Legit Hausa ta zakulo wasu daga cikin sharhin a kasa:

sadia_nas ta yi martani:

"Na yi crushing kan mutumin nan, har dai na hakura da yanzu shi ne Uban ‘ya’ya na "

Kara karanta wannan

Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin

elegant_glitz_sparkle ta rubuta:

"Yau kam lower your gaze dinnan,,da mata akeyi"

zinariyah_spa ta ce:

"Masha Allah. Abincin wani gubar wani. Duk namiji mai gashi a fuska haka ba dani ba."

spytro_kids ta ce:

"Mazan arewa sun bar dakin "

teemamzakari ta yi maryani:

"Nikuwa wlh abunda bantabayi ba kenan waishi crushing haka kawai."

k_t_z_clothing_08066401709 ta ce:

"Wannan itache the most expensive babbar riga A kasar hausa sunanta BULLA "

batoul_emporium:

" ya hadu no be lie. Astaghfirullah"

Mufti Menk ya gabatar da Lakca a taron murnar cikar Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki.

A wani labarin, Shahrarren Malamin addinin Musulunci a duniya, Mufti Isma'il Menk, ya gabatar da muhadara a taron cikar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Shekara 15 akan Karagar Mulki.

A jawabin da Masarautar ta saki a shafinta, Mufti Menk ya yi jawabi ne kan muhimmancin zaman lafiya.

Wannan taro ya gudana ne a dakin taron Conference Hall dake Kasarawa Sokoto.

Kara karanta wannan

So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng