'Yan sanda sun ceto malaman UNIAbuja da aka sace, an kama 'yan bindiga
- Rahotanni sun bayyana cewa, an ceto malaman jami'ar Abuja da aka sace a jerangiyar gidajen jami'ar ta farkon makon nan
- Hukumar jami'ar ta tabbatar da ceto malaman, kana ta bayyana godiya da jinjinawa ga jami'an tsaro da wadanda suka taimaka
- A halin da ake ciki, jami'an jami'ar na kan hanyar dauko malaman da aka sacen a ranar Talata domin tabbatar da lafiyarsu
Abuja - Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ceto malaman nan hudu da iyalansu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su da safiyar ranar Talata a gidanjensu na jami’ar Abuja.
Jami'in kula da al'amuran dalibai na jami'ar ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:
"Wadanda aka sace a UniAbuja an ceto su, ba a samu rauni ba, ba a biya kudin fansa ba. An kama mutane da yawa masu hannu Alhamdulillahi!!!"
Da take tabbatar da ceto malaman jami'ar, hukumar jami'ar da kanta ita ma ta wallafa a shafinta na Facebook cewa:
"Addu'armu ta karbu. Don Allah a taya ni godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Zan yi muku karin bayani daga baya, don kawai na sanar da ku cewa danginmu na UofA suna cikin farin ciki a yau tare da warware wannan mugunyar satar mutanenmu. Kamar yadda na rubutu a yanzu, muna kan hanyar dauko su kuma mu samar musu kulawar gaggawa don tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya."
Hakazalika, hukumar ta kuma jinjina da yabawa jami'an tsaro da suka yi kokarin ganin an ceto malaman da iyalansu.
A cewar sanarwar:
"Dole ne a yaba wa kwararrun Sashin Tsaronmu. Muna godiya ga tawagar tare da sojoji, 'yan sanda, DSS da duk wadanda suka yi aiki don ganin hakan ya faru."
A baya 'yan sanda sun karyata rahoton ceto wadanda aka sace
Kafin tabbatar da ceto malaman, a baya rundunar yan sandan birnin tarayya ta karyata rahotannin cewa an yi nasarar ceto mutane shida da yan bindiga suka yi garkuwa da su a gidajen malaman jami'ar Abuja.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan na FCT, Josephine Adeh ce ta bayyana hakan, gidan talbijin na AIT ta rahoto.
Adeh wacce ke martani ga wani sashi na labarai da ya nakalto wani ma'aikacin jami'ar yana tabbatar da ceto mutanen a Abaji, hanyar babban titin Abuja-Lokja da taimakon yan sanda da yan banga ta bukaci yan jarida da su guji yada labaran karya.
Asali: Legit.ng