Wata sabuwa: An kutsa shafin intanet na gwamnatin jiha ana ta damfarar masu neman aiki

Wata sabuwa: An kutsa shafin intanet na gwamnatin jiha ana ta damfarar masu neman aiki

  • Gwamnatin jihar Delta ta gargadi jama'a kan wata sabuwar kalar damfarar da aka bullo da ita
  • Gwamnatin ta ce an yi kutse a wata kafar yanar gizon gwamnati, inda aka tallata allon daukar aiki
  • Gwamnati ta ce a yi watsi da wannan tallan, kana ta yi Karin bayani kan yadda take daukar aiki

Delta - Gwamnatin jihar Delta ta yi watsi da wani tallan da aka yi ta yanar gizo na daukar ma’aikata a jihar, inda ta ce tallan na bogi ne Kuma yaudara, Punch ta ruwaito.

A ranar Larabar da ta gabata ne wasu da ake zargin 'yan kutse ne suka sanya fom din daukar aiki a shafin yanar gizon hukumar kula da ma’aikata ta jihar Delta, inda suka bukaci masu nema su sayi fom din shiga ma’aikatar daukar ma’aikata da karin girma ta jihar.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

Wata sabuwa: An kutsa shafin intanet na gwamnatin jiha ana ta damfarar masu neman aikin gwamnati
Taswirar jihar Delta | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mayar da fom din na dauke da sharadi na biyan kudi Naira 8,500 a asusun bankin hukumar ma'aikata na Unity Bank mai lamba 0010840393.

Wata sanarwa da daraktan yada labarai, Misis Theresa Oliko, ta fitar a ranar Alhamis, ta ce hukumar ma’aikata ta jihar Delta ba ta da izini daga gwamnan jihar don gudanar da duk wani aikin daukar ma’aikata.

Hakazalika inji sanarwar, gwamnati ba ta sanya wani talla a kan haka ba, haka kuma ba ta baiwa kowa izinin daukar ma’aikata ba.

A cewar sanarwar:

“Hukumar ba ta tallata daukar ma’aikata ko wasu ayyukan ta ta yanar gizo ba.
"Kada wani ya biya komai a cikin asusun bankin da aka ambata a cikin wannan tallan na karya ta yanar gizo."

Daraktan ya bayyana tallan a matsayin na bogi sannan ya shawarci jama’a da su yi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Karancin albashi: Mun maida lamarinmu ga Ubangiji inji Malamai da Ma’aikatan jihar Kogi

Abdurrassheed Bawa: Barayi suna amfani da Bitcoin wajen sace kudi a duniya

Abdulrasheed Bawa, shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ya ce kudaden intanet sun zama kyakkyawan zabi ga mutanen da ke gudanar da hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba, TheCable ta ruwaito.

Bawa ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, a taron kasa da kasa na Cambridge karo na 38 kan laifukan tattalin arziki, mai taken, 'Laifin Tattalin Arziki: Wa Ya Biya kuma Wa Ya Kamata Ya Biya Farashi?'

Cibiyar Adana Bayanai ta Duniya kan Tsararrun Laifukan Tattalin Arziki (CIDOEC) a Kwalejin Jesus ta Jami'ar Cambridge a Burtaniya ce ta shirya taron.

Ku koyi sana'a babu aikin da gwamnati za ta baku, inji wani sanata ga 'yan NYSC

A baya, Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Majalisar Dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ya shawarci membobin matasa 'yan bautar kasa da su hakaka kwarewar sana'a a maimakon tsammanin samun aikin gwamnati bayan hidimarsu ta shekara guda.

Kara karanta wannan

Bayan lafawar tawagar Gana a Benue, wasu muggan makasa sun fito da sabon salon kisa

Basiru ya ba da shawarar ne a cikin wata sanarwa mai taken, "Ba da gudummawa ga tattalin arziki ta hanyar habaka kwarewar sana'a," wanda wakilin jaridar Punch a ranar Alhamis 9 ga watan Satumba ya samu a babban birnin tarayya Abuja.

Basiru, a cewar sanarwar, ya yi magana ne a shirin habaka kwarewa da kasuwancin da aka shirya wa membobin bautan kasa a sansanin Koyar da Masu Yi wa Kasa Hidima a Ede, Jihar Osun, ranar Laraba 8 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.