Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

  • Wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe jami'an yan sanda hudu a jihar Anambra
  • Harin wanda ya afku a safiyar yau Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, yana zuwa ne yan kwanaki kafin zaben gwamnan jihar
  • Sai dai zuwa yanzu ba a ji ta bakin rundunar yan sandan ba kan al'amarin

Ekwusigo, Anambra - Yan kwanaki kafin zaben gwamna a jihar Anambra, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe jami'an yan sanda hudu a garin Oraifite da ke karamar hukumar Ekwusigo na jihar.

Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, bayan maharan sun bude wuta a kan jami'an tsaron, jaridar PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar gini a Legas ya karu zuwa 36

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Harin ya kara haifar da fargaba a tsakanin jami'an tsaro da ke gudanar da aikin zabe da kuma mazauna jihar.

An kuma tattaro cewa tsagerun sun yi awon gaba da makaman jami'an tsaron da suka kashe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Garin Oraifite yana kimanin kilomita 46 zuwa Awka, babbar birnin jihar.

Zuwa yanzu ba a san takamaiman adadin mutanen da suka mutu ba a harin.

Da aka tuntube shi don ji ta bakin shi, jami'in hulda da jama'a na sashi na 13, DSP Nkeiruka Nwude, wanda ke kula da lamuran zabe, ya nemi a tuntubi kakakin rundunar yan sandan Najeriya, CP Frank Mba.

Sai dai kuma, wayar tarho din Mba yana kashe a lokacin da aka tuntube shi domin tabbatar da harin.

Wata majiya da ke kusa da yankin wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa an kwashi wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti mafi kusa a yankin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi garkuwa da tsohon Shugaban NPA a jihar Kano

'Yan bindiga sun bindige jami'an yan sanda a jihar Ribas

A wani labarin kuma, mun kawo cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wasu jami’an ‘yan sanda biyu da ke aiki a ofishin rundunar na Mile One da ke Diobu, Port Harcourt, jihar Ribas, The Cable ta rahoto.

Wani ganau ya bayyana cewa an bindige jami'an tsaron ne a yayin da suke aikin tsayarwa tare da binciken motoci a unguwar Okija da ke yankin, rahoton Daily Trust.

Shaidan ya ce 'yan bindigar wadanda ke a cikin wata mota, sun afka wa jami’an tsaron da suka mutu sannan suka harbe su bayan sun yi gab da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng