2023: Dattijan Arewa sun yi mi'ara koma baya, sun ce za su yi aiki tare da sauran yankuna

2023: Dattijan Arewa sun yi mi'ara koma baya, sun ce za su yi aiki tare da sauran yankuna

  • A ranar Laraba kungiyar dattawan arewa ta sauya ra’ayin ta akan maganar da ta yi a baya dangane da shugabancin kasa a shekarar 2023 inda ta ce yanzu za ta yi aiki da sauran yankunan da ke Najeriya
  • Kakakin kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata takarda bayan kammala taro da shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi, ya ce sun yanke shawarar ne don a samu nagartattun shugabanni a 2023
  • Kungiyar ta bayyana yadda su ka yi taron ta kuma bayar da shawara akan duba yayin gyara akan kundin tsarin mulkin Najeriya, a rushe hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha

Kungiyar dattawan arewa a ranar Laraba ta sauya ra’ayin ta dangane da matsayar arewa a shugabanci a shekarar 2023, inda ta lashi takobi akan arewa za ta yi aiki da sauran yankunan Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

The Punch ta ruwaito yadda kungiyar dattawan ta ce za ta yi hakan ne don tabbatar da an samar da shugaba wanda zai kawo gyara ga kasa baki daya.

2023: Dattijan Arewa sun yi mi'ara koma baya, sun ce za su yi aiki tare da sauran yankuna
2023: Dattijan Arewa sun yi mi'ara koma baya, sun ce za su yi aiki da sauran yankuna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Kungiyar ta bayyana hakan ne bisa ruwayar Punch ta wata takarda wacce kakakin kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya saki bayan yin wani taro da shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi.

A yadda takardar ta zo, a taron sun kawo batun duba akan rushe hukumar zabe mai zaman kan ta ta jiha inda su ka ce ya kamata a gyare-gyaren kundin tsarin mulkin Najeriya a yi hakan.

Kungiyar ta shawarci ‘yan arewa akan yin rijista

Wani bangare na takardar ya bayyana cewa:

“Kungiyar ta sara wa ‘yan Najeriya wadanda su ka jajirce wurin kawo gyara akan tsarin siyasar mu. Yanzu ya rage ga ‘yan siyasa da sauran shugabanni su yi amfani da damar nan don samar da shugabanni ma su nagarta.

Kara karanta wannan

Shugaban CAN: Farashin kuɗin fansa ya ƙaru a Kaduna sakamakon rufe hanyoyin sadarwa da gwamnati ta yi

“NEF ta kula da yadda jam’iyyar PDP da APC su ka zama jam’iyyu 2 mafi shahara a kasar nan, inda ta ce ‘yan Najeriya za su karu idan wasu jam’iyyun su ka samu.
“NEF ta na jiran ganin an samar da wasu jam’iyyun. Ci gaba da aiki da hukumar zabe ta jiha mai zaman kan ta ya na ci gaba da lalata siyasa. Don haka kungiyar ta bayar da shawarar rushe ta.”

Har ila yau, kungiyar ta shawarci ‘yan Najeriya musamman ‘yan arewa da su yi rijista kuma su yi shirin zaben nagartattun shugabanni a zaben 2023.

Sun yi dubi akan halin rashin tsaron da kasa ta ke ciki inda ta ce arewa maso gabas ne ta fi fama da Boko Haram. Sannan matsalar garkuwa da mutane ta fi tsananta a arewa inda IPOB ta addabi kudu ma so gabas.

Kakakin ya kara da cewa talauci da rashin shugabanci mai kyau ne babban matsalar kasar nan kuma shi ne silar rashin tsaron.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

A wani rahoton kun ji cewa Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.

Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: