Malamin addinin musulunci ya yi garkuwa da dan uwansa, ya nemi a lale masa miliyoyin kudin fansa a Katsina
- Wani malamin addinin musulunci a jihar Katsina ya yi garkuwa da ɗan uwansa kuma ya nemi a ba shi kuɗin fansa
- Rundunar yan sandan jihar ta samu nasarar damƙe malamin, Jamilu Idris, wanda aka gano ya na da ɗalibai dake koyon karatu a wurinsa
- Tuni dai Idrsi ya amsa laifinsa kuma ya tabbatar da ya nemi mahaifin yaron ya biya miliyan N5m kuɗin fansa
Katsina - Rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ta cafke wani malami, Jamilu Idris, bisa zargin sace ɗan uwansa, Umar Farouk Kabir, ɗan shekara huɗu.
This Day ta rahoto cewa, Malamin dan kimanin shekara 39, ya fito ne daga Sabon-Fegi na ƙauyen Yankara, karamar hukumar Faskari, ya sace yaron tun 9 ga watan Oktoba.
Malam Idris, wanda aka gano yana da ɗalibai 41 a ƙarkashinsa, suna koyon karatun Alƙur'ani, ya yi garkuwa da yaron ne bayan ya jawo shi.
Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isa, ya bayyana wanda ake zargin tare da wasu mutum 13 ranar Laraba da yamma, inda yace malamin ya nemi a biya shi miliyan N5m kudin fansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ina malamin ya sace yaron?
Isah ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya sace ɗan uwan nasa ne a gidan mahaifinsa dake karamar hukumar Funtua, ya ɗauke shi zuwa Dutsen-Alhaji, dake yankin Abuja.
Premium times ta rahoto Kakakin yan sandan yace:
"A ranar 25 ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 11:00 na safe, jami'ai sun damke wani Jamilu Idris, ɗan shekara 39 daga Ƙauyen Yankara."
"Idris malamin addinin musulunci ne, ya jagoranci garkuwa da ɗan uwansa, Umar Farouk Kabir, ɗan shekara 4."
"Yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana yadda ya ziyarci gidan kawunsa a Funtua, ya kuma yi amfani da lemu wajen sace yaron."
Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ya faru
Shin Malamin ya nemi kuɗin fansa?
Kakakin rundunar yan sandan ya ƙara da cewa Malam Idris ya tuntuɓi kawun nasa ya biya kuɗin fansa miliyan N5m.
"Wanda ake zargin ya amince cewa ya nemi kuɗin fansa Naira Miliyan N5m amma mahaifin yaron yace N500,0000 zai iya biya."
A wani labarin kuma Wasu yan ta'adda da ake zargin mayaƙan kungiyar ISWAP ne sun hallaka jami'an yan sanda biyu da soja guda ɗaya a jihar Borno
Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da yan ta'addan suka yi kokarin kutsa wa garin Malamfatori, jami'an tsaron suka tarbe su aka yi musayar wuta
Garin Malamfatori dai na ɗaya daga cikin yankunan jihar Borno da yan Boko Haram suka maida hedkwatar su a baya.
Asali: Legit.ng