A karon farko, Miyagun yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta da dare a Taraba, mutum 7 sun mutu
- A karon farko wasu miyagun yan bindiga sun kai hari kauyen Naga, dake karamar hukumar Lau, jihar Taraba
- Maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutum 7 tare da jikkata wasu da dama
- Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya musanta cewa Naga a cikin jihar Taraba take
Taraba - Mutum 7 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka farmaki ƙauyen Naga, karamar hukumar Lau, jihar Taraba, da daren ranar Talata.
Dailytrust ta ruwaito cewa yan bindigan a kan mashina, sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare.
Daga shigar su, yan bindigan ba su yi wata-wata ba suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Maharan sun hallaka aƙalla mutum bakwai yayin da suka jikkata wasu adadi mai yawa a harin, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya daga ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa jim kaɗan bayan yan bindigan sun aikata wannan ta'addancin, sai suka gudu zuwa cikin daji.
A cewarsa wannan shine karo na farko da ƙauyen su ya fuskanci harin yan bindiga, waɗan da ba'a san ko su waye ba.
Me yan sanda suka ce game da harin?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya bayyana cewa Ƙauyen Naga, yana ƙarƙashin jihar Adamawa ne, ba Taraba ba.
A jawabinsa yace
"Ya kamata ku sani cewa ƙauyen da aka kai harin Naga, yana cikin jihar Adamawa ne, ba ƙaramar hukumar Lau, jihar Taraba ba."
A wani labarin kuma Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato, sun hana yan majalisu shiga
Rundunar yan sanda ta ɗauki matakin kwace zauren majalisar dokokin jihar Filato saboda rikicin shugabanci.
Rikici dai yaƙi ci yaƙi cinyewa a majalisar tun bayan tsige kakakin majalisar, Ayuba Abok, tare da maye gurbinsa da Yakubu Sanda.
Asali: Legit.ng