Sheikh Gumi ya sake magana kan yan bindiga, ya soki gwamnatin Buhari kan kokarin ayyana su yan ta'adda
- Sheikh Ahmad Gumi ya sake jaddada bukatar a yi wa yan bindiga afuwa kuma a inganta rayuwarsu
- Malamin ya jima yana gargaɗin gwamnatin tarayya kada ta yi kuskuren ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda
- A cewarsa ɗaukar wannan matakin zai sa su haɗa kai da Boko Haram, ISWAP kuma hakan zai jefa yan arewa cikin mummunan yanayi
Kaduna - Shahararren malamin addinin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ƙara jaddada matsayarsa cewa yi wa yan bindiga afuwa ne kaɗai hanyar kawo ƙarshen zubar da jinin mutane a Arewa.
Dailytrust ta rahoto Gumi na cewa ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda zai ƙara haifar da wasu matsaloli ne na ta'addanci.
Malamin ya yi wannan furuci ne a wurin sanya marayu rukuni na uku a shirin samar musu da ilimi, kula da lafiya kyauta, wanda gidauniyar musulunci a Kawo ta ɗauki nauyin shiryawa.
Me ya dace gwamnati ta yi wa yan bindiga?
Sheikh Gumi ya shawarci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari, kada ta zama silar ƙarin kashe-kashen mutane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Malam Gumi yace:
"Idan har akwai wata hanya da zata dakatar da zubar da jini, zai fi kyautuwa a yi musu kwatankwacin abinda aka yi wa mayaƙan Niger Delta."
"Sun kasance suna fasa bututun mai da zubar jinanen mutane, amma a shirye suke su aje makamansu idan za'a musu afuwa da ɗaukar nauyinsu, inaga za'a iya yi wa yan bindiga haka."
"Mun gana da su kuma a shirye suke su aje makamansu. Amma idan sun daina kuma ba'a samar musu da ilimi ba, da kuɗin da zasu kula da kansu, zasu koma gidan jiya ne."
Zasu ƙara ƙarfi idan aka ayyana su yan ta'adda - Gumi
Danagane da shirin FG na ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda, Malamin yace:
"Idan aka ayyana su yan ta'adda za'a haifar da wata matsala ne, su masu laifi ne da basu san komai ba, idan aka maida su kamar Boko Haram da ISWAP, zasu iya haɗa kai da su."
"Dole sai an kula wajen kokarin magance masu laifi jahilai, zamu yaƙe su da makami idan akwai bukatar hakan amma yanzun sulhu shi yafi alkhairi."
A wani labarin kuma An fara zaro gawarwakin mutane daga gini mai hawa 21 da ya rushe a Najeriya
Jami'an hukumar agaji NEMA sun samu nasarar gano gawar mutum uku daga cikin dogon ginin da ya rushe a jihar Legas.
Hakanan an kuma ceto wasu mutum uku da suke da sauran numfashi a gaba, suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu.
Asali: Legit.ng