Janyewar ruwa, rashin tsaro, ambaliya da abubuwa 5 za su jawo karin tsadar abinci a 2022

Janyewar ruwa, rashin tsaro, ambaliya da abubuwa 5 za su jawo karin tsadar abinci a 2022

  • Hasashe yana nuna cewa kayan abinci za su iya yin matukar tsada a shekarar 2022 da za a shiga.
  • Daga cikin abubuwan da za su jawo wannan matsala akwai janyewar ruwan sama da ambaliya.
  • Haka zalika an saye iri da takin zamani da tsada, sannan rufe kasuwannin kauye ya jawo tsadar abinci,

Nigeria - Wani bincike da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa akwai yiwuwar kayan noma da abinci su kara tsada a kakar wannan shekara da za a shiga.

A irin wannan lokaci a shekarar bara, ana saida buhunan shinkafa da masara a kan N11000 da N9000. A yau kuwa ana saida su a kan N20000 da N19000.

Haka zalika mudun waken suya da aka saya a bara kan N300 ya zama N400 a shekarar nan. Akwai manoman da ba su samu komai ba saboda ruwa ya dauke.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

Wani manomi yake cewa an saida buhun wake a kan N70, 000 a shekarar bana. Masana suna ganin babu mamaki a shekarar badi tsadar wake ya zarce haka.

‘Yan kasuwa sun fara asarar kudinsu

‘Yan kasuwa suna kukan sun yi asarar kudinsu a wannan shekara saboda sun kashe kudin mota, sun je gonakin kauye, amma ba su iya samun kayan gona ba.

Ganin yadda sababbin hatsin suka yi tsada a karshen damina ya sa ake ganin watakila farashin ya tashi. Manoma suna kukan cewa sun saye iri da tsada a bana.

Manomi
Wata gona a Najeriya Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

Damina ta tsaya, ana kashe kudin ban-ruwa

Daga cikin dalilan da suka jawo shinkafa da masara ba su yi sauki ba, akwai matsalar janyewar ruwan sama, wanda hakan ya jawo karancin kayan abincin.

Kara karanta wannan

Jigo a kudu ya gano hanyar lallabar 'yan Arewa su mika mulki kudu a 2023

Karancin ruwan saman ya jawo mutanen da suke kusa da ruwa sun fara yin ban-ruwa domin a shayar da shinkafa da dawa da sauran abincin da aka noma.

Taki da iri sun yi tsada a shekarar nan

Rahoton yace manoma sun ci buri da kayan gonansu a bana saboda an saye takin zamani da tsada. Hakan zai kara taimakawa wajen tsadar kayan abinci.

A jihar Kaduna, rufe kasuwannin wasu kauyuka da aka yi ya haddasa tashin farashin hatsi. Karancin kaya a kasuwa ya sa dole kayan noma suke tsada.

A wasu jihohi an gamu da ambaliyar ruwan sama da damina, wanda hakan ya jawo manoma suka tafka asara mai yawa, hakan ma zai iya jawo tsadar abincin.

Wata matsalar ita ce rashin tsaro wanda ta sa mutane da-dama suka kauracewa gonakinsu a bana. 'Yan bindiga sun hana manoma yin shuka a shekarar nan.

Farfesa Wole Soyinka ya caccaki salon APC

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

Kwanakin baya aka ji Farfesa Wole Soyinka ya na ta yin kaca-kaca da gwamnatin tarayya, yace ana ji, ana gani, Najeriya tana wargajewa yau a gaban idanunsu.

Farfesan yace duk mai jiran mafita daga gwamnatin nan, bai kama hanya ba domin shugaban kasa Muhammadu Buhari bai san yadda zai gyara kasar nan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng