Cikin hotuna, jiragen yaƙin NAF sun yi wa taron ƴan Boko Haram ruwan wuta, sun kashe 37 a Sambisa

Cikin hotuna, jiragen yaƙin NAF sun yi wa taron ƴan Boko Haram ruwan wuta, sun kashe 37 a Sambisa

  • Dakarun sojojin saman Nigeria a karkashin Operation Hadin Kai (OPHK) sun yi nasarar halaka yan ta'adda 37, sun kuma jikkata wasu
  • Hakan ya biyo bayan wani samame ne da sojojin suka kai wa yan ta'addan a yankin Sambisa yayin da suka taru don yin wani taro
  • Hakazalika sojojin kasa na OPHK sun ragargaji tarin wasu yan ta'dda da motocci masu bindiga hudu bayan sojojin sama sun hange su

Borno - A kalla 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram 37 ne jiragen yakin sojojin saman Nigeria, NAF, suka kashe yayin luguden wutan da suka yi musu a dajin Sambisa.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria, Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Facebook.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro da shugabannin tsaro sun dira Borno kan sabbin harin ISWAP

Cikin hotuna, jiragen yaƙin NAF sun yi wa taron ƴan Boko Haram ruwan wuta, sun kashe 37 a Sambisa
Yan ta'addan ISWAP a wurin taronsu a Sambisa. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cikin hotuna, jiragen yaƙin NAF sun yi wa taron ƴan Boko Haram ruwan wuta, sun kashe 37 a Sambisa
Jiragen yaƙin NAF sun yi wa taron ƴan Boko Haram ruwan wuta, sun kashe 37 a Sambisa. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Birgejiya Janar Nwachukwu ya kuma ce wasu da dama cikin yan ta'addan sun jikkata yayin harin da sojojin suka kai.

Mr Nwachukwu ya ce:

"Gamayyar dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) suna cigaba da ragargazan yan ta'adda a arewa maso gabas, a safiyar ranar Lahadi 30 ga watan Oktoban 2021, sojojin sun hangi motocci masu bindiga shida na tafiya a dajin Sambisa, daga bisani aka gansu kusa da Yuwe.
"Daga baya motoccin sun tafi wani wuri a daji, inda wasu yan ta'addan daban suka tarar da su, a wani yanayi da ya yi kama da taro.
"An gano yan ta'addan Boko Haram/ISWAP fiye da 50 sun taru wurin taron. Bayan tabbatar da wurin taron, OPHK ta tura jiragen yaki biyu sun yi luguden wuta cikin dare, nazarin da aka yi da kuma majiyoyi daga kauyen sun nuna cewa fiye da yan ta'adda 37 sun mutu yayin da wasu suka jikkata."

Kara karanta wannan

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

A wani cigaban kuma, a yayin da jiragen yakin ke komawa sansanin su sun hangi wasu motocci masu bindiga hudu misalin kilomita shida a yammacin Bama. Nan take suka sanar da sojojin kasa wurin da motoccin suke, su kuma suka tafi suka ragargaje su.

Sanarwar ta Nwachukwu ta ce hadin gwiwa tsakanin sojojin saman da na kasa tare da taimakon wasu hukumomin tsaron ya nuna muhimmancin hadin kai a yaki da ta'addanci.

Daga karshe ya ce OPHK za ta cigaba da jajircewa har sai ta ga bayan 'yan ta'addan.

Labari da ɗuminsa: An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa

A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.

An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da motocci masu bindiga 15 suna can sun kai hari Damboa

A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164