Ci gaba: Buhari zai kaddamar da wani katafaren jirgin ruwan soji da aka kera a Najeriya

Ci gaba: Buhari zai kaddamar da wani katafaren jirgin ruwan soji da aka kera a Najeriya

  • 'Yan Najeriya sun kera jirgin ruwa, Shugaba Buhari zai kaddamar da jirgin a watan Disamba
  • A cewar hukuma, wannan shine jirgi na uku da hukumar sojin ruwan Najeriya ta kera
  • Shugaba Buhari ya ji dadin haka, ya ce ya kamata 'yan Najeriya su yi alfahari da wannan aikin

Abuja - The Cable ta ruwaito cewa, Shugaba Buhari zai kaddamar da wani jirgin ruwan da aka kera a bakin tekun Najeriya a watan Disamba 2021.

Awwal Gambo, babban hafsan sojin ruwa, ya ce ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa, ranar Lahadi, ta gayyatar shugaban kasar a hukumance ne domin kaddamar da jirgin ruwan da ‘yan asalin kasar suka kera.

VON ta ruwaito cewa, ganawar tasu ta zo ne gabanin ficewar Shugaba Buhari zuwa Glaslow domin halartar wani taro.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya

Ci gaba: Buhari zai kaddamar da wani katafaren jirgin ruwan soji da aka kera a Najeriya
Lokacin da ake tattauna batun jirgin ruwa | von.gov.ng
Asali: UGC

Jirgin na daya daga cikin uku da ma'aikatan sojin ruwan Najeriya ke kerawa a Legas.

Babban hafsan sojin ruwan ya ce:

"Jirgin ruwan zai karu kan wasu jiragen ruwa da muke da su don kare yankin tekun Najeriya daga masu sata a teku, fashin teku, shigo da kaya ba bisa ka'ida ba da duk sauran laifukan kan ruwa".

Da yake mayar da martani, shugaba Buhari ya ce kammala jirgin wata nasara ce da ya kamata al'ummar kasar su yi alfahari da ita.

A kalamansa:

"Abin alfaharin mu ne a matsayinmu na kasa cewa za mu iya kera wani abu tun daga tushe har zuwa karshe, daga tashar jiragen ruwanmu. Don haka abin alfahari ne a gare mu."

Gambo wanda ya ki bayyana kudin da aka kashe wajen kera jirgin ya ce dai an kashe kudi da yawa.

Kara karanta wannan

Jerin tituna 21 da za su ci makudan kudade, kuma gwamnatin Buhari ta amince a yi

A cewarsa;

"Ba kamar lokacin da kuke samun masu siyar da kayayyaki na kasashen waje don kerawa ko samar da jirgin ba. Yana ragewa kasar da yawa da kuma ci gaba, muna sa ran yin hakan cikin kankanin lokaci."

Babban hafsan na sojin ruwa ya ce wasu kasashe sun nuna sha’awar hada gwiwa da Najeriya wajen kera jiragen ruwa da kuma kula da su.

Ya kara da cewa:

"Muna da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a shirye suke kuma suna son hada gwiwa da mu wajen kera jiragen ruwa da kuma kula da su.
“Muna da tashar jirgin ruwa na Badagry da ke son gina tashar jirgin ruwa a Badagry. Har ila yau, a shirye suke su hada gwiwa da mu wajen kula da jiragen da kuma gine-gine kuma galibin kasashen da ke gabar tekun Yamma za su ba mu tallafi."

Wasu kere-keren Najeriya

A wani labarin, Najeriya ta yi fiye da fitar da danyen mai kadai da wasu kayayyakin amfanin gona a shekarar 2020, ba tare da wani abin a zo a gani ba a bangaren fasahar zamani, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara

A matsayinta na kasa mai dogaro da shigo da kayayyaki, kasar ta yi shekara da shekaru tana kokarin samar da kudaden shiga ta kasashen waje da kuma habaka darajar Naira, kasar na kuma fama da gibin cinikayya da ake samu.

Yayin da take shigo da komai daga kayan fasahar zamani zuwa waken soya zuwa abun tsokale hakori, babban abin da Najeriya ke fitarwa shine danyen mai. Hakanan ana sayar da koko, Kashu da wasu kayan amfanin gona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.