Ana saura mako daya zabe Gwamna, yan majalisa 3 sun sauya sheka APC
- Jam'iyyar APC ta samu babban karuwa ana saura kasa da mako guda zaben gwamnan jihar Anambra
- Dan majalisar wakilai tare da yan majalisan dokokin jiha biyu suka sauya sheka daga APGA rana guda
- Gwamnan Yobe ya ce lallai yanzu ya fara tabbata jam'iyyar APC za ta lashe zaben Anambra
Awka - Jam'iyya mai rike da gwamnati a jihar Anambara, All Progressives Grand Alliance (APGA), ta yi babban rashi sakamakon sauya shekan wani dan majalisar wakilan tarayya.
Hanarabul Chukwuma Umeoji mai wakilatar mazabar Aguata a majalisa ta koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Hakazalika wasu yan majalisar dokokin jihar biyu tare da dimbin mabiyansu sun koma APC tare a Hanarabul Umeoji, rahoton Leadership.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban kwamitin rikon kwaryar APC kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da kansa ya tarbi wadannan sabbin yan jam'iyyar.
Buni a jawabinsa ya siffanta Umeoji matsayin babban dan siyasa kuma dawowarsa ya kara musu tabbacin cewa APC zata lashe zaben gwamnan.
A cewar Buni,
"APC na tare da kai da mabiyanka, kuma zata kare muradunku na siyasa a koda yaushe."
"Za ta ji dadin dukkan wani abu da 'yayan jam'iyyar ke ji."
An tattaro cewa Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, da dan takarar gwamnan karkashin jam'iyyar APGA sun yi kokarinsu na ganin dan majalisan bai sauya sheka ba amma abin ya ci tura.
Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra
Dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.
Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.
Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.
Asali: Legit.ng