Dalilin da yasa har yanzun Gwamnatin Buhari ba ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda ba

Dalilin da yasa har yanzun Gwamnatin Buhari ba ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda ba

  • Ministan tsaron ƙasar nan, Bashir Magashi, ya bayyana cewa ba hakanan kawai gwamnati zata fito ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda ba
  • Ministan yace akwai matakai da ya zama wajibi gwamnati ta bi kafin ɗaukar wannan matakin, kuma a yanzun an kusa kammala wa
  • Gwamnatin Buhari na cigaba da fuskantar matsin lamba daga mutane cewa ta gaggauta ayyana yan fashin daji a matsayin yan ta'adda

Borno - Ministan tsaro, Bashir Magashi, yace gwamnatin tarayya ta ƙi ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda ne saboda sai ta bi ƙa'idoji da dokoki.

The Cable ta rahoto cewa wannan matakai da gwamnati take ƙoƙarin bi shine musabbabin jan kafar da ake ganin ta na yi wajen ayyana hakan.

Da yake jawabi ga manema labarai a Maiduguri ranar Jumu'a, Ministan yace akwai matakan da za'a kammala cika su kafin a ayyana su a matsayin yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu

Ministan Tsaro, Bashir Magashi
Dalilin da yasa har yanzun Gwamnatin Buhari ba ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda ba Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewarsa ba hakanan kawai gwamnatin tarayya zata fito ta ayyana ba kamar yadda mutane suke ta kiraye-kirayen a yi, kamar yadda channels tv ta rahoto.

Ana cigaba da kira ga gwamnatin shugaba Buhari da ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda daga kowane sassan ƙasar nan.

Wane matakai ne wannan?

A jawabinsa Ministan tsaron yace:

"Bamu ayyana su a matsayin yan ta'adda bane saboda akwai matakai kafin yin hakan."
"Da zaran an bi waɗan nan matakan, zamu ayyana su a matsayin yan ta'adda. Amma a halin yanzun muna jiran a kammala cika waɗan nan matakan."

Me yakai ministan Maiduguri?

Magashi ya ƙara da cewa ya kawo ziyara Maiduguri ne tare da hafsoshin tsaro domin duba inda aka kwana a yaƙin da ake da yan ta'adda a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa

Ya kuma bayyana gamsuwarsa da nasarorin da jami'an tsaro suke samu, inda ya ƙara da cewa tawagarsa zata gana da kwamandoji domin ɗaukar mataki na gaba.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 5 a wani sabon hari da suka kai jihar Katsina

Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari Kauyen Dangeza a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun hallaka mutum biyar yayin da wasu da dama suke asibiti domin kula da lafiyarsu bayan harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262