Na ranste da Al-Qur'ani ba zan nemi tazarce ba, Shugaba Buhari

Na ranste da Al-Qur'ani ba zan nemi tazarce ba, Shugaba Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wasu yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya ranar Juma'a
  • Buhari ya bayyanawa yan Najeriyan cewa ko kadan ba zai nemi yin tazarce bayan karewa wa'adinsa a 2023 ba
  • Ya yi alkawarin inganta rayukan yan Najeriya cikin kimanin watanni goma sha takwas da suka rage masa

Makkah, Saudiyya - Shugaba Muhammadu Buhari ya rantse da Al-Qur'ani mai girma cewa wa'adinsa na karewa ba zai nemi ya yi tazarce kan kujerar mulkin Najeriya ba.

Buhari ya bayyana haka ne a ganawar da yayi da wasu yan Najeriya mazauna Kasar Saudiyya yayinda yake shirin bankwana da kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya

Shugaban kasar ya bada tabbacin cewa wa'adinsa na karewa zai sauka daga mulki.

Yace:

"Na rantse da Al-Qur'ani mai tsarki cewa zanyi mulki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada kuma zan tafi idan wa'adi na ya kare."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babu Tazarce. Bana son wani ya rika magana akan tazarce. Ba zan yarda da hakan ba."

Ba zan nemi tazarce ba, Shugaba Buhari
Na ranste da Al-Qur'ani ba zan nemi tazarce ba, Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Depositphotos

Cikin dan lokaci na da ya rage zan taimakawa rayuwar yan Najeriya

Shugaban kasan ya bayyana cewa cikin dan lokacin da ya rage masa, zaiyi kokari wajen inganta rayuwar yan Najeriya.

"Cikin watanni 18 da suka rage na wa'adi na, zan yi duk abinda zan iya na inganta rayukan yan Najeriya, zan yi ne don bauta ga kasar," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng