Kotu ta ɗaure malaman addinin musulunci 2 da aka kama da sassan jikin bil’adama a Kwara
- Bayan an kwashe shekaru 4 ana shari’a, wata kotu a jihar Ilorin ta daure malaman addinin musulunci, Folorunsho Abdulwahab da mahaifin sa, Suleiman Babatunde Olaitan bisa mallakar sassan jikin dan-adam
- Alkalin kotun, Bio Saliu, ya yanke wa Abdulwahab shekaru 4 a gidan gyaran hali yayin da mahaifin sa zai yi zaman watanni 4 a gidan yari sannan za a ci shi tarar N3,000
- An yanke wa Abdulwahab hukuncin ne bayan kama shi da laifin tono gawar abokin sa bayan an birnr shi da na kwana 5, warin da aka ji daga gidan malamin ne ya ja hankalin jama’a
Kwara - Bayan kwashe shekaru 4 ana shari’a, kotu ta yanke wa malaman addinin musulunci, Olaitan Folorunsho Abdulwahab da mahaifinsa, Suleiman Babatunde, hukuncin zama a gidan yari bisa mallakar sassan jikin bil-adama.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda malamin ya yi amfani da gawar wani Suleiman Saka bayan tono ta daga kabari.
Alkalin kotun, Bio Saliu ya yanke wa Abdulwahab shekaru 4 a gidan yari yayin da mahaifin sa zai yi watanni 4 sannan ya biya harajin N3,000 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai laifin, Abdulwahab ya tono gawar abokin bayan rufe shi da tsawon kwana 5 bayan an birne shi duk don ya yi tsafi da shi.
An maka karar su inda aka gabatar da su gaban alkali Bio Saliu sakamakon kulle-kulle da kuma mallakar sashin bil’adama ba bisa ka’ida ba wanda ya ci karo da yanki na 97, 342 da 219 na Penal Code.
Mahaifin mamacin ne ya kai korafin
Rahoton farko shi ne wanda wani Alhaji Aliyu Baba Alapa na anguwar Onilu, Oloje a Ilorin ya kawo korafi ga ofishin ‘yan sanda na garin.
Wanda ya kai korafin ya ce ya samu bayani akan yadda aka tono kabarin dan sa, Suleiman Saka a anguwar su ta Olaje kuma aka yi awon gaba da gawar.
Sakamakon warin da mutane su dinga ji daga gidan da aka ajiye gawar ne ya sa su ka yanke shawarar binciken gidan.
An ga kan mutum, hannaye 2 da kafafu 2 a cikin wani bokiti wanda aka boye a wani daki a cikin gidan.
An samu labarin yadda Abdulwahab, Oladimeji, Jelili, Weidi da wasu su ka wuce da sauran sassannin jikin mamacin a cikin wata mota kirar Honda Accord.
An kama Olaitan a cikin wadanda su ka tsere bayan aukuwar lamarin, a Ajuwon da ke jihar Ogun.
Ya yi bayani dalla-dalla akan yadda su ka hada kai da sauran abokan shu’umancin sa wurin aiwatar da mummunan aikin.
Tun 2018 aka kama su kuma a ka sakaya su a gidan yari.
Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba
A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.
‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.
Asali: Legit.ng