Aisha Buhari ta bayyana burinta na tallafawa mata da kananan yara su samu ilimi

Aisha Buhari ta bayyana burinta na tallafawa mata da kananan yara su samu ilimi

  • Aisha Buhari ta dauki aniyar yaki da don kare hakkin mata da kananan yara mata tare da ba su ilimi
  • Ta bayyana haka ne yayin da ta karbi bakuncin wasu masana harhada magunguna da suka ziyarce ta a Abuja
  • Ta bayyana yadda gidauniyarta ta gina wata makaranta a jihar Borno don tallafawa mata a jihar

Abuja - Daily Nigerian ta ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa a shirye ta ke ta karfafa hadin gwiwa da sauran masu hannu da shuni don bayar da tallafin da ake bukata a ci gaban ilimin mata da yara.

Aisha Buhari ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, a lokacin da ta karbi bakuncin mambobin kungiyar masu harhada magunguna ta Najeriya (NAPPSA), daga kasar Amurka, wadanda suka kai mata ziyara a Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

Aisha Buhari ta sha alwashin yaki don kare hakkin mata da yara, tare da basu ilimi
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari | Hoto: Aisha Buhari
Asali: Depositphotos

Ta ce gidauniyar ta, ta hanyar hadin guiwar abokan huldar ci gaba, ta bayar da tallafi ga mata, matasa da sauran iyalai marasa galihu, musamman a fannin kiwon lafiya, gina asibitocin haihuwa da inganta ilimin yara mata.

Uwargidan shugaban kasar ta kuma shaida wa maziyartan cewa gidauniyar Aisha Buhari ta gina kwaleji a Maiduguri da nufin tallafa wa yara mata wajen neman ilimi musamman yaran da iyayensu suka mutu a rikicin Boko Haram, inji The Guardian.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta:

“Kafa Kwalejin Future Assured a Maiduguri, jihar Borno kwanan nan, an yi shi ne don samar da ilimi ga yara ‘yan mata wadanda rikici ya shafa.
“Wannan tallafin da aka bayar shine jagorar abin da za mu iya yi tare don tallafa wa wadannan matasan kwakwale don su samu kyakkyawar makoma duba da kalubalen da ke fuskantar ilimin ’ya’ya mata.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

"Halin samar da ingantaccen kiwon lafiya da ilimin 'ya'ya mata a makaranta da kuma a gida yana fuskantar kalubale sosai."

Don haka ta bukaci masu ruwa da tsaki da su daina mai da hankali kan sha’awar tabbatar da yanayi mai kyau ga mata da ‘ya’ya mata domin cimma burinsu a nan gaba.

A nata martanin, shugabar NAPPSA, Teresa Pounds, ta yaba da kokarin uwargidan shugaban kasar wajen daukar nauyin mata, matasa da yara.

Pounds ta ce sun hallara a fadar gwamnatin ne domin bayyana goyon baya ga kokarin uwargidan shugaban kasar wajen bayar da tallafi ga mata da kananan yara a Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, NAPPSA kungiya ce ta masana harhada magunguna da masana kimiyya da ke da hedkwata a Amurka da ta kunshi mambobi daga Amurka da Kanada.

An kafa kungiyar ne a shekara ta 2007 a kokarin samar da wani dandali ga masana kimiyyar harhada magunguna na Najeriya a cikin kwarewa don bayyana hanyoyin tallafawa ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin tituna 21 da za su ci makudan kudade, kuma gwamnatin Buhari ta amince a yi

Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

A wani labarin, jerin sunayen 'yan takarar hadin kai da ake zargin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta amince da su a matsayin 'yan takarar jam'iyyar APC na jihar Adamawa ne aka yanke hukuncin sun yi nasara a zaben shugabancin APC na jihar.

SaharaReporters ta rahoto cewa dukkan masu takarar da sunayensu ke cikin jerin hadin kai nan ba da jimawa ba za a bayyana su a matsayin wadanda suka yi nasara a taron gangamin jam'iyyar da aka yi a ranar Asabar.

Yayin da al'amura ke tafiya ta hanyar tsarin zabe, kuri'un da aka kada ya zuwa yanzu sun nuna cewa 'yan takarar da Uwargidan Shugaban kasa ke tallafawa sune wadanda aka zaba a taron gangamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.