Ba zan yarda ba, Kakakin majalisar dokokin Plateau da aka tsige ya bude nasa majalisar
- Hanarabul Nuhu Abok ya lashi takobin cewa har yanzu shine Kakakin majalisar dokokin jihar Plateau
- Dan lokaci bayan tsigeshi, dan majalisar ya bude nasa kwarya-kwaryar majalisar a wani dakin taro
- Gwamnan jihar Plateau ya bayyana cewa yayi mamaki lokacin da ya samu labarin tsige Kakakin
Jos, Plateau - Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Plateau, Kakakin da aka tsige ya ce ba zai yarda ba.
Tsigaggen Kakakin majalisar Nuhu Abok, ya bude nasa zauren majalisar a wajen majalisa yan sa'o'i bayan tsigeshi da aka yi, rahoton TVC News.
Ba tare da bata lokaci, ya shirya zama tare da wasu a waje da wadanda ke goyon bayansa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majalisar dokokin jihar Filato ta tsige shugaban majalisar, Honorabul Abok Ayuba Nuhu
Majalisar dokokin jihar Filato ta tsige kakakinta, Honorabul Abok Ayuba Nuhu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Rahoto ya bayyana cewa an maye tsohon kakakin da Honorabul Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana, karamar hukumar Bassa, jihar Filato.
Mambobin majalisa 16 cikin 24 na majalisar dokokin ne suka kada kuri'ar amince wa da tsige shugaban nasu a zaman majalisa na yau Alhamis.
Channels TV ta rahoto cewa Mambobin majalisa na jam'iyyar APC mai mulki ne suka tsige shugaban da sanyin safiyar Alhamis.
Gwamna Lalong ya yi martani, ya nuna kaduwa kan tsige kakakin Filato
Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya yi martani kan tsige Abok Ayuba a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar.
Ya bayyana cewa ya yi mamaki matuka a kan al’amarin.
Asali: Legit.ng