Bidiyoyin Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

Bidiyoyin Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Makkah domin yin Umrah bayan kammala taro a Riyadh da ke Saudiya
  • A bidiyon da Buhari Sallau ya wallafa, an ga shugaban kasan a Masallacin Annabi S. A. W tare da tawagarsa
  • Garba Shehu ya bayyana cewa, Buhari ya kwarara addu'o'in zaman lafiya da na ingantar tsaro ga Najeriya da duniya baki daya

Saudi Arabia - A ranar Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karasa Birnin Makkah da ke kasar Saudiya domin yin Umrah.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a wata takarda da ya fitar, ya ce Buhari da tawagarsa sun yi wa Najeriya da jama'ar ta fatan samun zaman lafiya da tsaro.

Kamar yadda Shehu ya bayyana, ya ce addu'o'in har da na fatan habakar tattalin arziki bayan annobar korona domin karuwar kasar nan da jama'ar ta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari

Buhari ya yi Umrah a Saudiyya, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya
Buhari ya yi Umrah a Saudiyya, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce mataimakin gwamnan yankin, Yarima Sa'ud Al-Faisal ne ya karba shugaban kasar a filin sauka da tashin jiragen sama na Yarima Muhammad Abdulaziz da ke Madina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun kwashe tsawon lokaci a cikin Masjid Annabawi inda suka dinga addu'o'i da karatun Al-Qur'ani mai girma.

A ranar Litinin shugaban kasa Muhammadu ya bar birniin Abuja inda ya sauka a birnin Riyadh domin halartar wani gagarumin taron kasuwanci a kasar Saudi Arabia.

A ranar Laraba, ya tsaya a Madinah inda ya yi sallolin dare tare da yin addu'o'i tare da tawagarsa. Ya roki zaman lafiya da tsaro a fadin Najeriya da duniya baki daya.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin majalisar malaman Kano: Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng