Miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari jihar Zamfara, Sun kashe Mutane

Miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari jihar Zamfara, Sun kashe Mutane

  • Wasu yan bindiga sun sake kai sabon hari yankin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi a ƙauyen Yanbuki, inda suka kashe aƙalla mutum 7
  • Wani mazaunin garin, Garba Musa, yace maharan sun kwashi kayan abinci, sannan sun sace dabbobi akalla guda 1,500

Zamfara - Tsagerun yan bingida sun sake kai farmaki ƙauyen Yanbuki dake ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Punch ta ruwaito cewa maharan sun hallaka aƙalla mutum bakwai sannan sun kwashi kayan abinci, tare da yin awon gaba da dabbobi sama da 1,500.

Wani ɗan asalin ƙauyen, Garba Musa, wanda ya zanta da manema labarai a Gusau, yace adadi mai yawa na yan bindigan sun mamaye ƙauyen ranar Talata da daddare.

Miyagun yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari jihar Zamfara, Sun kashe Mutane Hoto: tvcnews.tv
Asali: UGC

Musa ya bayyana cewa da isowar su ƙauyen, sai suka buɗe wuta kan duk wanda suka gani domin tsorata mutanen dake garin.

Kara karanta wannan

An kuma kai hari: Miyagun yan bindiga sun hallaka akalla mutum 6, sun sace wasu da dama a jihar Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamrin ya faru

Musa yace:

"Suna isowa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi saboda haka kowa ya fara gudun neman tsira da rayuwarsa."
"Daga nan kuma sai suka fara shiga gida-gida suna neman kayan abinci da dabbobi, sannan kuma duk shagon da suka gani suna fasa shi su kwashi kayan abinci."
"Hakanan kuma sun yi awon gaba da dabbobin kiyo sama da 1,500, wanda suka haɗa da shanu, awaki da tumaki."

Mutum nawa yan bindigan suka kashe?

A cewarsa bayan yan bindigan sun gama abinda suka zo yi, an gano mutum 7 sun rasa ransu sannan wasu da dama sun jikkata, kamar yadda Channels ta ruwaito.

"Mun yi jana'izar mutum 7, kuma adadin waɗanda suka mutu ba zai wuce haka ba, domin wasu sun tsere cikin daji domin tsira da rayuwarsu."

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin yan sandan jihar, SP Muhammed Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, yace:

"Kwamishinan yan sandan jihar ya tura ƙarin jami'an yan sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya."

A wani labarin kuma kun ji cewa Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja

Aminiya ta rahoto cewa Hakimin yankin Adogon, Alhaji Sa'idu Abubakar da ɗan uwansa, Alhaji Salihu Abubakar, sun rasa ransu ne a harin da ake tunanin na ɗaukar fansa ne.

Tun a baya dai, wasu mahara sun buɗe wa mutane dake sallar Asuuba wuta, inda suka ƙashe aƙalla mutum 18 tare da sace wasu a garin Maza-Kuka, jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262