Dalibai sun yo hayar ‘yan daba domin su lallasa malamansu, an jikkata wasu

Dalibai sun yo hayar ‘yan daba domin su lallasa malamansu, an jikkata wasu

  • 'Yan daba sun kai hari kan malaman makarantar gwamnati ta Community High School, Ijoun, da ke karamar hukumar Yewa ta arewa a jihar Ogun
  • An tattaro cewa daliban makarantar ne suka yo hayar 'yan iskan domin su fatattaki malaman nasu daga makarantar
  • Yanzu haka wasu na kwance a asibiti sakamakon raunuka da suka samu a harin

Ogun - Daliban makarantar gwamnati ta Community High School, Ijoun, da ke karamar hukumar Yewa ta arewa a jihar Ogun, sun yo hayar wasu ‘yan daba domin kai hari tare da fatattakar malamansu daga makarantar.

Lamarin wanda ya afku a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, yana zuwa ne mako guda bayan wasu daliban makarantar gwamnati ta Kajola, Ibooro, sun aikata irin haka ga malamansu.

Kara karanta wannan

Da Dumi: An rufe kwallejin Ilimi ta tarayya da ke Yola saboda zanga-zangar ɗalibai

Dalibai sun yo hayar ‘yan daba domin su lallasa malamansu, an jikkata wasu
Dalibai sun yo hayar ‘yan daba domin su lallasa malamansu, an jikkata wasu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta, ta fada ma jaridar Punch cewa ‘yan daban sun isa harabar makarantar dauke da makamai sannan suka farma malaman, inda suka raunata su.

Majiyar ta ce, maharan sun kai farmaki makarantar da misalin karfe 10:45 na safiyar ranar Litinin sannan suka yi amfani da makamai irin su adduna da gatari kan malaman Stephen Oyelekan da Kayode Olatunji, kafin suka tsere.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kuma nuna cewa an shigar da kara ofishin ‘yan sandan Eegua yayin da wadanda abun ya rutsa da su ke asibiti don jinya.

An kuma tattaro cewa shugabannin makarantun sakandaren, Mista Sowunmi da Kayode Amusa, sun sanar da Adele na garin Ijoun, Cif Olaleye Emmanuel, da shugaban Amotekun na yankin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce koda dai ya samu labarin faruwar lamarin, amma ba a sanar da shi ba a hukumance.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

An rufe kwallejin Ilimi ta tarayya da ke Yola saboda zanga-zangar ɗalibai

A wani labari na daban, mun ji cewa zanga-zangar dalibai da ya janyo rikici ya tilasta rufe kwallejin ilimi ta gwamnatin tarayya, FCE, da ke Yola a jihar Adamawa.

Wani rahoto daga SaharaReporters ta ce daliban suna zanga-zanga ne saboda mawuyacin halin da suke ciki a makarantar da ya hada da rashin ruwa. Daga bisani zanga-zangar da aka fara ta lumana ta janyo rikici.

SaharaReporters ta rahoto cewa zanga-zangar da kaceme ne a yayin da sojoji da sauran jami'an tsaro suka fara fatattakar daliban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng