Gwamnan jihar Kano ya samu lambar yabon zakaran yaki da rashawa kuma mai amana

Gwamnan jihar Kano ya samu lambar yabon zakaran yaki da rashawa kuma mai amana

  • An karrama gwamnan jihar Kano bisa namijin ayyukan da yake yiwa al'umma
  • Hukumar tabbatar da ana kashe kudi yadda ya kamata ce tayi masa wannan karrama
  • Lambar yabon ya hada da na yaki da rashawa da kuma kwarewa wajen shugabanci

Hukumar Kula da yadda ake kashe kudin kasa wato (Fiscal Responsibility Commission) ta karrama Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da lambar yabo.

A jawabin da hadimin daukar hoton gwamnan, Aminu Dahiru, yayi, yace a alanta Gwamna Ganduje a mastayin jajirtaccen shugaba a fannin gudanar da gwamnati a bayyane kuma bisa amana

Hakazalika an karramashi kan yadda yake alkinta kudaden Jiha wajen gudanar da ayyukan cigaba da jin dadin al'ummar jiharsa.

Hukumar ta ce ya zama dole a yabawa Gwamnan bisa rawar gani wajen gudanar da mulki wanda yake a bude da kuma amfani da kudin gwamnati wajen samar da ababan more rayuwa ga ‘yan jihar.

Kara karanta wannan

ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja

Gwamnan jihar Kano ya samu lambar yabon zakaran yaki da rashawa a Najeriya
Gwamnan jihar Kano ya samu lambar yabon zakaran yaki da rashawa a Najeriya Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban hukumar, Barista Victor Muruako ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jiga-jigan Hukumar su ka kai wa Gwamnan ziyara a ofishinsa da ke fadar gwamnati a yau Litinin.

Me Gwamna Ganduje yace?

Gwamna Ganduje ya yi maraba da jami'an hukumar sannan ya yaba musu bisa shirya taron wayar da kai akan tsantseni da rikon amana wajen sarrafa kudaden gwamnati sanar ya bayyana aniyar sa ta yin aiki da su.

A lokacin ziyarar Gwamnan yana tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Hon. Ali Haruna Makoda da kwamishinoni da shugaban riko na Hukumar Karbar Korafe Korafe, Barr. Balarabe Mahmud da sauran jami'an gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng