Ministan Buhari ya bayyana abun da ka iya haddasa yakin duniya na uku
- Lai Mohammed, ministan labarai da al’adu ya yi jan hankali a kan yada labaran karya
- A cewar ministan, labaran karya shine zai haddasa yakin duniya na uku idan har ba a yake shi ba
- Ya ce a yanzu mutane sun fi ba shafukan yanar gizo muhimmanci fiye da gidajen talbijin da radiyo
Abuja - Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya gargadi al’umman kasar a kan yada labaran karya, inda ya ce hakan na iya haddasa yakin duniya na uku.
Mohammed ya fadi hakan ne a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan labarai domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa na 2022.
Ministan ya ce sigar da ake amfani da ita wajen yada labarai a yau ta canza matuka, jaridar The Cable ta rahoto.
Ya ce hanyoyin samun labarai a shekaru 30 da suka gabata sune ta talbijin da radiyo, inda ya kara da cewa mutane a yanzu sun fi ba soshiyal midiya muhimmanci wanda yace anan ne ake yada labaran karya cikin sauki, Daily Post ta kuma rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
“Mutane a yanzu, basa karanta jaridu, basa kallon talbijin, sai soshiyal midiya. Kuma ya fi kowanne tsada; a nan ne ake da makiyan da ba a gani da idanu, suna can a koda yaushe.
“Da labaran karya a yau da kuma rashin bayar da bayani yadda yake – ina yawan fadi a nan cewa labaran karya ne zai haddasa yakin duniya na gaba.
“Za ku ga cewa hatta kasar US da kan yi alfahari da kanta kan yancin labarai a yanzu tana dasa ayar tambaya a kan rawar ganin da soshiyal midiya ke takawa.
Yaki da labaran karya
A koda yaushe Mohammed kan nuna damuwarsa kan annobar da ke tattare da labaran karya da kuma hatsarurrukan shi.
Hakan ya sa gwamnatin tarayya ta dage wajen ganin an kafa dokar da za ta sanya idanu kan kafafen sadarwa na yanar gizo.
A wani taron jin ra’ayin jama’a a watan Yuni, Mohammed ya nemi majalisar wakilai da ta yi wa hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBC) gyaran fuska domin bata damar daidaita kafafen sada zumunta da na yanar gizo.
Wannan ya kasance ne bayan NBC ta bukaci dukkanin shafukan soshiyal midiya da kafafen sadarwa na yanar gizo da ke aiki a Najeriya su nemi lasisin yada labarai.
Lai Mohammed ya yi magana game da sabuwar manhaja da za ta maye gurbin Twitter a Nigeria
A wani labarin, mun ji a baya cewa Lai Mohammed, Ministan labarai da al'adu, ya bukaci yan Nigeria su kirkiro da shafin dandalin sada zumunta da zai maye gurbin Twitter a Nigeria.
Mohammed ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai na tarayya, a ranar Laraba 23 ga watan Yuni don kare dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi wa Twitter a cewar OAK TV.
Mohammed ya shawarci yan Nigeria su yi amfani da damar da ta samu bayan dakatar da Twitter su kirkiro manhajar da yan Nigeria za su rika amfani da ita.
Asali: Legit.ng