Lai Mohammed ya yi magana game da sabuwar manhaja da za ta maye gurbin Twitter a Nigeria

Lai Mohammed ya yi magana game da sabuwar manhaja da za ta maye gurbin Twitter a Nigeria

  • Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi laifi ba bisa dakatar da Twitter
  • Mohammed ya ce dakatar da ayyukan Twitter ya bawa yan Nigeria masu basira damar nuna bajintarsu a bangaren fasaha
  • Wakilan gwamnatin tarayya sun fara tattaunawa da kamfanin dandalin sada zumuntar na Twitter game da dakatarwar

Lai Mohammed, Ministan labarai da al'adu, ya bukaci yan Nigeria su kirkiro da shafin dandalin sada zumunta da zai maye gurbin Twitter a Nigeria.

Mohammed ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai na tarayya, a ranar Laraba 23 ga watan Yuni don kare dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi wa Twitter a cewar OAK TV.

Lai Mohammed ya bukaci a rika sa ido a dandalin sada zumunta.
Lai Mohammed ya bukaci a rika sa ido a dandalin sada zumunta. Hoto: Ma'aikatan Labarai da Al'adu ta Nigeria
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da Duminsa: Tsohon gwamnan babban bankin Nigeria ya lallasa abokan hammayarsa ya zama dan takarar gwamnan APGA

Ministan ya karfafawa yan Nigeria gwiwa su rika kirkirar manhajarsu

Mohammed ya shawarci yan Nigeria su yi amfani da damar da ta samu bayan dakatar da Twitter su kirkiro manhajar da yan Nigeria za su rika amfani da ita.

Ministan ya ce:

"Ina ganin wannan dama ce mai kyau ga yan Nigeria masu basira su duba yadda za a yi su kirkiro manhajar da za ta maye gurbin Twitter."
Ya kuma shawarci yan Nigeria su guji amfani da VPN domin bi ta bayan gida suna shiga Twitter. Mohammed ya ce masu amfani da VPN na fuskantar hatsarin a sace musu bayanai."

KU KARANTA: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Ministan ya ce:

"Shawarar da zan bawa duk wani mai amfani da VPN shine ya dena domin hakan barazana ce ga bayanan ku har da asusun ajiyar bankin ka."

Majalisa ta saka baki kan rikicin Twitter da FG

The Punch ta ruwaito cewa majalisar wakilai na tarayya ta umurci kwamitocinta na sadarwar, sharia, labarai da al'adu da tsaron kasa su yi bincike kan dakatarwar da FG ta yi wa Twitter su bada rahoto cikin kwanaki 10.

A wani labarin daban, Fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, suna bakin ciki kan dakatar da Twitter ne saboda ya rage damar da suke da shi na yaɗa 'labaran ƙarya', rahoton The Cable.

A ranar 4 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta dakatar da shafin dandalin sada zumuntan kan ikirarin cewa ana amfani da shi wurin raba kan ƴan ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164