Mun damke manyan mutane da muke zargi da hannu a fasa gidan yarin Oyo, Gwamna
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa hukumomi na tsare da wasu gaggan mutanen da ake zargi da fasa gidan yari
- Gwamnan yace mutane na da saurin fara yaɗa jita-jita, amma a halin yanzun ana cigaba da gudanar da bincike
- Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, yace jami'ai sun kamo mafi yawa daga cikin fursunonin da suka tsere
Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, yace wasu manyan yan tada zaune tsaye sun shiga hannu bisa zargin hannu a fasa gidan yari a jihar.
The Cable ta ruwaito cewa wasu tsagerun yan bindiga sun ɓarke gidan yari a jihar Oyo, inda suka saki fursunoni sama da 500.
Da yake jawabi lokacin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru, tare da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, gwamnan yace har yanzun ana cigaba da bincike.
Sai dai Makinde bai bayyana sunayen manyan waɗanda ake zargin ba, kuma bai fayyace ko suna cikin fursunonin da suka tsere ba.
Amma jita-jitar dake yawo ta nuna cewa daga cikin su akwai wani sanannen makashi, Sunday Shodipe, da wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Iskilu Wakili.
Muna tsare da manyan da muke zargi - Gwamna
A jawabin gwamnan yace:
"Muna tsare da manyan yan ta'adda da muke zargi a nan, mutane na da saurin fara yaɗa jita-jita amma abinda zan iya cewa ana cigaba da bincike."
"Ina kira ga mutane su kwantar da hankulansu, muna fama da ƙalubale da dama a faɗin ƙasa, yan bindiga, yan fashi da sauransu."
Zamu magance su ne kaɗai idan muka damke mutanen dake haɗa kai da su, kuma shine abinda muke kokarin yi."
Fursunoni nawa aka kamo bayan sun tsere?
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa cikin fursuna 907 da suka gudu, yanzun an sake kame 446 yayin da ake cigaba da neman sauran 392.
A wani labarin kuma Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari
Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki shahararren malamin nan na addinin kirista, Rabaran Ejike Mbaka, ya daina magana mara ɗaɗi akan shugaban ƙasa Buhari.
Shugaban gwamnonin yankin, Gwamna David Umahi, tare da rakiyar gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, na jihar Enugu , sune suka roki malamin amadadin sauran.
Asali: Legit.ng