Yadda 'yan fashi suka harbi mai shagon POS saboda kin basu kudi cikin dadin rai

Yadda 'yan fashi suka harbi mai shagon POS saboda kin basu kudi cikin dadin rai

  • 'Yan fashi sun dira shagon POS, sun saci kudi tare da harbin mai sana'ar POS a gwiwa
  • Lamarin ya faru ne ranar Asabar a jihar Oyo da misalin karfe 8 na dare a Ogbomosho
  • 'Yan sanda inji majiyoyi sun ki daukar mataki akai saboda zargin masu shagon da hannu a zanga-zangar #EndSARS

Oyo - 'Yan fashi da makami sun harbi wata mai sana'ar cire kudi da POS mai suna Dorcas a tashar Alade Mega da ke Garin Ogbomoso, Jihar Oyo a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa SaharaReporters cewa 'yan fashin sun isa shagon da misalin karfe 8 na dare lokacin da sauran ma'aikata suka kawo cinikinsu na yau da kullum zuwa hedikwatar kamfanin.

Ta bayyana cewa lokacin da mutanen uku dauke da makamai suka isa shagon, sun gabatar da kansu a matsayin ‘yan fashi, kuma sun nemi mai aikin da ta fito da dukkan kudin da ke shagon.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun kai sabon hari Yobe, sun sha ruwan wuta a hannun sojojin Najeriya

'Yan fashi sun harbi mai shagon POS saboda kin basu kudi cikin gaggawa
'Yan fashi | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar wanda abin ya faru a idonTa, an harbi Dorcas a gwiwa yayin da take kokarin rokon mutanen da ke dauke da makamai cewa ita ma'aikaciya ce kawai ba mai shagon ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce an kai batun ofishin 'yan sanda na Ogbomoso ta Kudu amma 'yan sandan da ke can suka bayyana zargin masu shagon sun goyi bayan zanga-zangar #EndSARS.

Shaidan da abin ya faru idonta ta ce:

“Sun nemi ta ba da cinikin da ta yi amma ta fara rokon su cewa ita mai aike ce kawai, duk da hakan, sun harbe ta kuma suka kwace N300,000 daga shagon.
"Bayan haka, mai shagon ya kai rahoton karar a ofishin 'yan sanda na Ogbomoso ta Kudu. Amma 'yan sanda suna zargin mu cewa mun ba da gudunmawa ga rashin tsaro a Najeriya saboda mun goyi bayan zanga-zangar #EndSARS.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

A karshen makon nan ne aka sake yin zanga-zangar #EndSARS a wasu sassan Najeriya don nuna kin jinin wasu bangarori na 'yan sanda.

Baya ga zanga-zangar #EndSARS, akan samu hare-hare da tashe-tashen hankula a yankuna daban na Najeriya ciki har da na 'yan aware a yankin Igbo da Yarbawa.

A makon da ya gabata ne aka zauna zaman kotu don sauraran kara kan Nnamdi Kanu, wani shugaban 'yan aware, inda ya musanta zargin da ake a kansa, The Cable ta ruwaito.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

A wani labarin, The Nation ta ruwaito cewa, an harbe jami’ai uku a cikin ofishin ‘yan sanda da ke Unwana, karamar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa jami’an da suka mutu akwai kwanstabul da sifetoci biyu.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Wani mazaunin Uwana, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce 'yan bindigar sun rufe fuska.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.