Sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin tsaronmu ba – Tukur Buratai

Sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin tsaronmu ba – Tukur Buratai

  • Tukur Buratai, jakadan Najeriya a jumhuriyar Benin ya ce ba zai yiwu kasar ta dogara kan sojoji ba kadai don magance matsalolin tsaro
  • Buratai ya kuma ce akwai bukatar samun ci gaba a arewa maso gabas don magance lamarin ta’addanci a yankin
  • Tsohon shugaban hafsan sojin kasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba, a wajen wani taro a garin Yola

Yola, jihar Adamawa - Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai main ritaya, ya bayyana cewa mataki na sojoji kadai ba zai iya magance matsalolin rashin tsaro ba a kasar nan.

Tsohon shugaban hafsan sojin kasar, ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 22 ga watan Oktoba, a garin Yola, babbar birnin jihar Adamawa, yayin wani taro a jami'ar Modibbo Adama.

Kara karanta wannan

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

Sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin tsaronmu ba – Tukur Buratai
Sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin tsaronmu ba – Tukur Buratai Hoto: Daily Asset Online
Asali: UGC

A cewar Buratai, rashin ci gaba a yankin Arewa maso Gabas shine babban abin da ke rura wutar ta'addanci da rashin tsaro a yankin, Daily Trust ta rahoto.

Don haka, ya ce dole sai an samu ci gaba a yankin na arewa maso gabas idan har ana so a magance lamarin ta'addanci a yankin, jaridar The Cable ta kuma rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Duk kasar da bata tabbatar da ci gaban mutanenta ba toh za ta fuskanci matsaloli na tsaro.
"Kada mu dogara a kan zabin sojoji kadai a matsayin hanyar magance matsalolin tsaronmu.Dole mu magance abubuwan da suka shafi tattalin arziki, zamantakewa, da siyasa.
"Rikicin diflomasiyyana na baya-bayan nan ya kara karfafa ra'ayina game da bukatar amfani da mafita ta sojoji, da kuma wanda ba na soji ba wajen shawo kan rikice-rikicen da ba a bukata."

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

Buratai ya kuma bayyana cewa lamarin na bukatar hadin kai, fahimtar siyasa, sadaukarwa da jajircewar gwamnati, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da duk masu ruwa da tsaki don takaita yawan kai hare-hare da kawo karshen rikicin.

Buratai ya yi nuni da cewa duk wanda ya dogara da sojoji kadai wajen magance ta'addanci kamar Boko Haram toh lallai zai ci gaba da fuskantar rashin tsaro.

Shugaban kasa daga arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addanci - Gwamna Fintiri

A wani labarin, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa zabar shugaban kasa daga yankin arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addancin da yankunan kasar ke fuskanta.

Fintiri, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Maxwell Gidado, ya bayyana hakan ne a taron karramawa na mujallar North East Star na 2021, inda aka bashi lambar yabo a matsayin gwamnan shekarar.

Gwamnan ya bayyana cewa ta’addanci a arewa maso gabas zai zo karshe a zangon farko na shugabancin kowani dan takara daga arewa maso gabashin kasar, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikici a APC yayin da aka rantsar da 'yan wani tsagi bayan taron gangami a Ribas

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng