Kotu ta yanke wa wani ɗaurin shekara ɗaya ba zaɓin tara saboda satar tankin ruwa na N35,000
- Kotu ta yanke wa wani mutum mai shekaru 39 hukuncin daurin shekara ba zabin tara
- An yanke wa Kazeem Papoola wannan hukuncin ne saboda satar tankin ruwa na N35,000
- Mai gabatar da karar ya kutsa gidan wani Mr Olatunde Tella ya sace tankin ruwan samfurin Geepee
Abeokuta - Wata kotun majistare mai zamanta a Abeokuta, a ranar Juma'a ta yanke wa wani mutum mai shekara 39, Kazeem Papoola hukuncin daurin shekara gida a gidan yari saboda satar tankin ruwa.
Yan sanda sun tuhumi Papoola, wanda ba a bada adireshinsa ba, da laifin kutse da kuma sata kamar yadda ya zo a ruwayar NAN.
Alkalin kotun, I.O. Abudu ya ce kotu ta sami Papoola da laifin ya kara da cewa masu shigar da karar sun gamsar da kotu cewa an aikata laifin.
Don haka, Abudu, ya yanke wa Papoola hukuncin daurin shekara guda daya a gidan gyaran hali ba tare da zabin biyan tara ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tunda farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Olakunle Shonibare ya shaida wa kotu cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Afrilu a Igbore road a unguwar Ijeja a Abeokuta.
Shonibare ya ce wanda aka yanke wa hukuncin ya kutsa gidan wani Mr Olatunde Tella ya kuma sace tankin ajiyar ruwa samfurin Geepee wanda kudinsa ya kai N35,000.
Mai gabatar da karar ya bayyana cewa laifin ya ci karo da sashi na 411(2) da 390(9) na kudin masu laifi na jihar Ogun ta shekarar 2006.
An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba
A wani rahoton, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.
Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.
An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.
Asali: Legit.ng