Yan jam'iyyar APC akalla 1000 sun kona tsintsiya a jihar Bauchi, sun koma PDP

Yan jam'iyyar APC akalla 1000 sun kona tsintsiya a jihar Bauchi, sun koma PDP

  • Yan jam'iyyar hamayya a karamar hukumar Dass sun sauya sheka PDP
  • Masu sauya shekan sun kona tsintsiya a cikin sauya shekar da aka yi
  • Manyan jiga-jigan siyasar PDP sun halarci taron

Jihar Bauchi - Akalla yan jam'iyyun adawa 1000 a karamar hukumar Dass a jihar Bauchi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) lokaci guda.

Mafi akasarin masu sauya shekan sun fita ne daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bayan zaben shugabannin jam'iyyar ta sake haddasa rikici cikin 'yayan jam'iyyar, Tribune ta ruwaito.

Sauran kuma sun fito daga jam'iyyun PRP, NNPP da APGA.

Shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Dass, Alh Sani Korau (Shattiman Dass) ya karbi bakuncinsu a taro na musamman da aka shirya a hedkwatar karamar hukumar.

Ya bayyana cewa dama tun asali babu yan adawa a karamar hukumar Dass saboda yayi farin cikin komawarsu.

Kara karanta wannan

Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban jam'iyyar, Bala Hadith; tsohon kakakin majalisar jihar, Sale Abubakar Dumba; kwamishanar Kimiya da Fasaha, Maryam Garba, da sauran su.

Yan jam'iyyar APC akalla 1000 sun kona tsintsiya a jihar Bauchi, sun koma PDP
Yan jam'iyyar APC akalla 1000 sun kona tsintsiya a jihar Bauchi, sun koma PDP Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

Me yasa suka sauya sheka?

Shugabannin masu sauya shekan sun bayyana cewa sun yanke shawaran komawa PDP ne saboda namijin ayyukan da gwamnatin Bala Mohammad ke yi.

Kwamishanan kananan hukumomin jihar, Abdulrazzak Nuhu zaki, ya bayyana farin cikinsa kuma yayi kira ga mutan Dass su goyawa gwamnan baya.

Zaku tuna cewa tsohon Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, kuma babban dan adawan gwamna Bala ya wakilci Dass a majalisa.

Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na da jajirtattun mutane da zasu iya shugabantan kasar nan a 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa

A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal sun bayyana niyyar takara a zaben shugaban kasa mai uwa.

Makinde ya bayyana hakan ne yayin jawabi a hirarsa a tashar ChannelsTV ranar Alhamis.

Gwamnan yace hanya daya tilo da zata ceci jam'iyyar PDP daga barkewa shine gwamnoninta su hada kai da juna gabanin zaben kasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng