Zargin kashe-kashe: Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske kan rikicin iyakar Bauchi da Gombe
- Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta yi martani a kan rahoton da ke cewa an kashe mutane a wani rikici tsakanin garuruwan da ke kan iyaka a jihohin Bauchi da Gombe
- Mai magana da yawun yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ya ce babu wanda aka kashe a rikicin sabanin yadda aka rahoto
- Wakil ya kuma bayyana cewa wasu mutane ne daga Gombe suka kai farmaki wasu gonaki a karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar Bauchi sannan suka yi harbe-harbe a iska
Bauchi – Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ba a rasa rai ko daya ba a yayin rikicin da ya wakana tsakanin garuruwan da ke kan iyaka a jihohin Bauchi da Gombe.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Bauchi a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.
Hakan martani ne ga rahotannin cewa an yi kashe-kashen rayuka bayan wasu al’ummomin Gombe sun kai farmaki wasu gonaki a karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar Bauchi.
Wakil ya yi bayanin cewa maharan sun yi harbe-harbe ne a iska, inda suka kuma lalata gonaki kafin suka bar wajen, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce bisa ga rahoton da rundunar ta samu, ba a kashe kowa ba a harin. Sannan ya ce rundunar ta tura jami’ai zuwa wajen da al’amarin ya afku kuma tuni zaman lafiya ya dawo a yankin.
Ya kuma ce za a gudanar da wani taro tsakanin gwamnonin Bauchi da Gombe, shugabannin garuruwan da abun ya shafa, sarakunan gargajiya da kuma shugabanni daga yankin, domin tattauna mafita da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin garuruwan, rahoton Punch.
Rundunar yan sanda ta bankaɗo waɗanda suke da hannu a kisan Sarakuna guda biyu
A wani labari na daban, kwamishinan yan sanda na jihar Imo, Rabiu Hussaini, ya zargi haramtacciyar ƙungiyar IPOB da mayaƙan ESN da kisan sarakuna biyu a jihar Imo.
The Nation ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun baɗe wa sarakunan gargajiya wuta a ƙaramar hukumar Njaba jihar Imo, mutum biyu suka mutu, ranar Talata.
Kwamishinan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, Michael Abattam, ya fitar ranar Laraba.
Asali: Legit.ng