Yanzu-yanzu: Ba mu da tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, MD na NRC ya magantu
- Manajan daraktan NRC, Fidet Okhiria, ya karyata rade-radin da ke yawo na cewa 'yan ta'adda sun kai wa jiragen kasa farmaki
- Okhiria ya ce har yanzu babu tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, ya alakanta lalacewar dogon da aikin mabarnata masu lalata kayan NRC
- A cewarsa, suna aiki tukuru wurin gyaran layikan dogon kuma akwai sa ran jiragen kasan su cigaba da aiki zuwa yammacin Alhamis
Manajan daraktan hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC, Fidet Okhiria, ya musanta rade-radin da ke ta yawo na cewa 'yan ta'adda sun kai wa jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna farmaki.
Okhiria wanda ya zanta da Daily Trust ta wayar salula, ya tabbatar da cewa wani sashi na layin dogon ne aka lalata.
Sai dai, ya alakanta lamarin da mabarnata masu lalata kayan gwamnati inda ya ce ana bincike domin bankado abinda ya faru.
"Da gaske ne an lalata layin dogo," yace tare da karawa da cewa bai tabbatar da cewa farmakin 'yan ta'adda ba ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce akwai yuwuwar mabarnata ne suka lalata dogon saboda a cikin kwanakin nan suna ta lalata kayayyakin hukumar NRC.
"Mun samu matsala da layin dogo amma muna gyarawa. Muna son komawa daukar fasinjoji a yau Alhamis da yammaci. Zai yuwu mu koma aiki.
“A safiyar yau Alhamis, jirgi daga Kaduna zuwa Abuja ya tashi, amma dole ta sa muka tsayar da ayyuka saboda lalatattun titunan har sai mun gyara," ya sake tabbatarwa.
Ya kara da tabbatarwa da Daily Trust cewa suna aiki tukuru wurin inganta tsaro a hanyoyin.
Muna cikin tafiya sai muka ji kara - Fasinjojin jirgin da aka kai wa hari sun bayyana halin da suka shiga
A wani labari na daban, fasinjojin jirgin da ake zaton 'yan bindiga sun kai wa hari a daren ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba a hanyar Kaduna zuwa Abuja sun bayyana halin da suka shiga.
Matafiyan sun bayyana cewa sai da suka shafe kimanin awa hudu a cikin dajin Allah inda suka yi cirko-cirko ba tare da sanin madafa ba.
Daily Trust ta rahoto cewa an ja jirgin kasan, wanda shine tashin karshe na ranar, zuwa tashar jirgin kasa na Rigasa da misalin karfe 2:00 na tsakar dare bayan an turo sabon jirgi daga tashar Idu da ke Abuja domin ceto fasinjojin da suka yi cirko-cirko.
Asali: Legit.ng