Zagayen Maulidi: Wahala ta kashe mutum daya, wasu goma sun sume a Abuja
- Wata matashiya mai suna Asma'u ta kwanta dama a yayin zagayen Maulidi a babbar birnin tarayya Abuja
- Hakazalika akalla mutum goma ne suka sume a wajen tattakin da aka yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad
- Ana zaton wahala da karancin kayan aiki ne ya haddasa faruwar mummunan al'amarin
Abuja - Wata ‘yar kungiyar agaji ta Munazzamatul Fityanul Islam ta yanke jiki ta fadi matacciya inda wasu 10 suka sume a yayin zagayen Maulidi da aka gudanar a Abuja.
A jiya Talata, 19 ga watan Oktoba ne daukacin al’umman Musulmi da suka hada da daliban Islamiyya, ‘yan kungiyoyin agaji da sauransu daga bangarori daban-daban na birnin tarayya suka yi tattaki a unguwannin Abuja.
Sun yi gangamin ne domin bikin zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu wakilcin ministan birnin tarayya, Malam Muhammdu Musa Bello a wajen taron.
Da take magana a kan lamarin, wata jagorar kungiyar da ke kula da yankin Kuje, Malama Sajida Bala Abdullahi, ta ce marigayiyar wacce aka ambata da suna Asma’u mai shekaru 20 ta fito ne daga yankin don halartan taron.
Malama Asma’u ta ce:
“Mun fara tattakin ne daga Mabushi da safe sannan muka doshi wajen taron tare da sauran ‘yan uwanmu ‘yan agaji da sauransu.
“Da na isa wajen taron ne na samu labarin cewa Asma’u ta yanke jiki ta fadi a hanya kuma an tabbatar da mutuwarta."
An tattaro cewa baya ga Asma’u, wasu ‘yan agaji 10 sun yanke jiki sun fadi a yayin zagayen. An kuma kwashe su zuwa asibiti.
Jagoran shirya taron, Dr Adamu Muhammadu Inuwa, ya bayyana cewa an shirya kawo karshen taron ne da misalin karfe 2:00 na rana amma aka tashi ba tare da shiri ba saboda lamarin.
Malam Muhammad Abani, ma’ajin kungiyar Jama’atu Ahbabul Rasul, reshen Abuja, ya alakanta faruwar al’amarin da karancin kayan aiki.
Ya ce:
“Zagayen ya fara ne da misalin karfe 7:00 na safe lokacin da wasu daga cikin ‘yan zagayen basu karya kumallonsu ba sannan da dama daga cikinsu sun kasance a tsaye na dogon lokaci suna jiran layi ya kai kansu zuwa wajen taron.”
Annabi na kowa ne: Faston da ya jagoranci kiristoci zuwa shagalin bikin Maulidi a Kaduna
A wani labarin, Kiristoci sun taya musulmai shagalin bikin Maulidi, haihuwar Annabi Muhammadu, SAW a jihar Kaduna a ranar Talata kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.
Mabiyan addinan biyu sun taru ne a Ranchers Bees Stadium da ke birnin jihar, inda ya ce taron zai taimaka wurin karfafa zumunci tsakanin addinai da al’adun.
Shugaban fastocin Christ Evangelical Intercessory Fellowship Ministries, Sabon Tasha, Fasto Yohanna Buru ne ya jagoranci Kiristocin wurin shagalin murnar haihuwar annabi Muhammad SAW.
Asali: Legit.ng