Gwamnatin tarayya ta soke hukumomin man fetur uku, kuma ta sallami shugabanninsu, ga jerinsu
1 - tsawon mintuna
- Gwamnatin tarayya ta soke wasu hukumomin man fetur guda uku
- Soke wadannan ma'aikatu ya biyo bayan kafa dokar ma'aikatar man fetir PIA
- Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana hakan a Abuja
Abuja - Bayan kafa dokar ma'aikatar man fetur, gwamnatin tarayya ta soke wasu hukumomin ma'aikatar guda uku lokaci guda.
Karamin Ministan arzikin man fetur, Chief Timipre Sylva, ya bayyana hakan ne yayin bikin ranstar da majalisun lura da hakar man fetur na kasa da ruwa a Abuja, ma'aikatar ta bayyana hakan a shafinta na Facebook.
Hukumomin sune:
1. Hukumar arzikin mai (DPR)
2. Asusun lamunin daidaita farashin man fetur (PEF)
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Hukumar sanya farashi da lura da farashin mai (PPPRA)
Ministan yace:
"Dokar da kanta ta soke dokar kafa DPR, dokar PEF, da dokar PPPRA. Yanzu ya bayyana karara babu wadannan hukumomin yanzu."
Bayan haka, gwamnatin tace an sallami dukkan shugabannin wadannan hukumomi amma ba za'a kori ma'aikatan hukumomin ba.
Asali: Legit.ng