Sabon rikici ya barke tsakanin mazauna Benue da Ebonyi, an sanya dokar ta baci
- Wani sabon rikici ya kunno kai tsakanin mazauna wani kauye tsakanin Benue da Ebonyi
- An rasa mutane yayin rikicin, lamarin da ya kai ga sanya dokar hana fita a wani yankin Benue
- An shawarci mazauna yankin da su zuba ido kan kara barkewar rikici domin wanzar da zaman lafiya
Benue - Rahoton Daily Trust na cewa, an sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a karamar hukumar Ado ta jihar Benue bayan sabon tashin hankalin da ya barke tsakanin wasu mazauna kauye a yankin.
Rahotanni a baya sun ce an rasa mutane tara a cikin garuruwan da ke kusa a yankin da ake rikicin tsakanin kananan hukumomi.
Shugaban Karamar Hukumar Ado, James Oche, ya sanar da dokar hana fita a ranar Lahadi 17 ga watan Oktoba a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Makurdi.
Oche ya ce matakin da ya dauka ya dogara ne ga matsalolin tsaro a gundumar Apa da ke karamar hukumar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma, an tattara daga mazauna yankin cewa an tsinci gawa da safiyar Lahadi.
Wannan lamarin ya biyo bayan sabon tashin hankali a yankin tsakanin al'ummomin karkara a kan iyakokin jihohin Benue da Ebonyi.
Shugaban ya shawarci mutane da su guji kowane irin yunkurin aikata laifi nan da nan ko kuma su girbi abin da suka shuka kamar yadda hukumomin tsaro a shirye suke don daukar matakai masu tsauri.
Oche, duk da haka, ya bukaci duk mutanen da ke zaune a gundumar Apa da ke karamar hukumar da su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton abubuwan da ake zargi na tsaro cikin gaggawa ga wuraren da suka dace.
Jihar Benue na daga cikin jihohin da ke fuskantar irin wadannan rikice-rikicen kabilanci da garkuwa da mutane har ma tsakanin makiyaya da manoma.
A watan Janairun bana, an sanya dokar ta baci a yankin Katsina Ala na jihar saboda yawaitar fashi da makami daga wasu tsageru, inji rahoton Channels Tv.
Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa
A wani labarin, Sahara Reporters ta ruwaito cewa, akalla sojojin Najeriya uku da mayakan Boko Haram 20 sun rasa rayukansu a ranar Asabar yayin da sojoji ke kokarin kwato garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
An ce maharan sun mamaye jerangiyar gidajen 777, a wajen birnin Maiduguri da misalin karfe 10:15 na daren Asabar.
Wani rahoton daban ya ce an gaggauta tura jirage masu saukar ungulu na rundunar sojin sama don hana maharan kwace yankin.
Asali: Legit.ng