Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara
- Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa yan fashin daji sun fara sako mutanen da suka kama saboda babu abincin ba su
- Dakta Abdullahi Shinkafi, mataimakin kwamitin tsaro, yace matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka suna haifar da ɗa mai ido
- Yace rashin sadarwa ta sa maharan na tura sako ta wasika, kuma jami'an tsaro na amfani da wannan damar wajen damke su
Zamfara - Mataimakin shugaban kwamitin nemo hanyoyin daƙile ayyukan yan bindiga a Zamfara, Dakta Abdullahi Shinkafi, yace yan fashin daji sun rasa abincin da zasu ciyar da mutanen da suka kama.
Channels tv ta ruwaito Shinkafi na cewa matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka sun saka yan ta'addan sako mutane ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Shinkafi ya yi wannan furucin ne yayin wata fira a Gusau, lokacin da yake yaba wa matakan daƙile yawaitar ayyukan ta'addanci a jihar.
Shinkafi yace:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Akwai wasu mutum 11 da mahara suka sace, sun sako ɗaya domin ya sanar da cewa sai an biya N200,000 a kan kowannen su."
"Kafin tattaunawa ta yi nisa yan fashin suka nemi a biya miliyan N20,000 kan kowane mutun ɗaya. Iyalan mutanen suka ƙi tura kuɗin, dole ta sa suka sako mutanen kyauta."
"A cewarsu babu abincin da zasu cigaba da ciyar da su. Saboda haka matakan suna haifar da ɗa mai ido."
Shin datse hanyoyin sadarwa yana taimakawa?
Shinkafi ya kara da cewa game da datse hanyoyin sadarwa, yan fashin dajin sun tura saƙon wasika zuwa ga mutanen Shinkafi da kuma sarkin Zurmi.
Ya bayyana cewa yan bindigan sun yi amfani da takardar shedar siyan babur wajen rubuta wasiƙa ga mutane domin neman kuɗin fansa.
Ya kuma tabbatar da cewa jami'an tsaro sun yi amfani da adireshin kamfani. mashin ɗin, wajen gano yan ta'addan kuma aka damƙe su.
A wani labarin kuma Hukumar Kwastam ta fallasa yadda yan sumogan shinkafa ke tallafawa yan bindiga a Katsina
Shugaban hukumar, Wada Chedi, yace da farko sun fara samun bayanan sirri amma daga bisani suka bi diddigin lamarin har suka tabbatar.
A cewarsa yan sumoga na ƙara wa tankin mai girma sannan su cikashi a gidan mai sukai wa yan bindiga.
Asali: Legit.ng