Wata Sabuwa: Matan jam'iyyar PDP Sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaba

Wata Sabuwa: Matan jam'iyyar PDP Sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaba

  • Mambobin jam'iyyar hamayya PDP sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa
  • Matan sun yi wannan kira ne ya yin wani taro da suka gudanar a sakateriyar jam'iyyar PDP ta ƙasa dake Abuja
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan PDP ta amince da shawarar kai kujerar shugabanta zuwa yankin Arewa

Abuja - Ya yin da babbar jam'iyyar hamayya PDP ke shirye-shiryen gangamin taronta na ƙasa, mambobin jam'iyyar mata sun nemi a basu kujerar mataimakin shuagaban jam'iyya na ƙasa.

Matan jam'iyyar na ganin yadda ake ta cece kuce kan yankin da ya dace a kai tikitin shugaban ƙasa, amma ba'a cewa komai game da su.

Channels tv ta rahoto cewa Mambobin PDP mata sun yi wannan kira ne a wani taro da suka gudanar a sakateriyar jam'iyyar PDP dake Abuja, ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

Matan jam'iyyar PDP
Wata Sabuwa: Matan jam'iyyar PDP Sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaba Hoto: rfi.fr
Asali: UGC

Daga wane yanki shugaban PDP zai fito?

Wannan kira dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP ya amince da shawarin kwamitin mulkin ƙarba-karba.

Kwamitin da PDP ta kafa domin nazari kan tsarin karba-karba, ya baiwa uwar jam'iyya shawarar ta maida kujerar shugabanta yankin Arewa

Matakan da PDP ta ɗauka, sun haɗa da duk wasu kujeru da mutanen kudu ke rike da su, zasu koma hannun yan arewa, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Yan Arewa sun sulhunta kansu

Kwanaki kaɗan bayan PDP ta sanar da wannan matakin, shugabannin PDP a Arewa suka zaɓi Sanata Iyorchia Ayu, a matsayin wanda suka amince ya taka takara daga yankin.

Babban gangamin taron PDP na ƙasa zai gudana ne a ranakun 30 da kuma 31 ga watan Oktoba, kamar yadda jam'iyyar ta tsara.

Kara karanta wannan

Matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi magana mai muhimmanci kan Matan Gwamnoni

A wani labarin na daban kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benuwai.

Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262